Ladduban da ake bi Allah ya amsa addu'a, Sheikh Aminu Daurawa

Ladduban da ake bi Allah ya amsa addu'a, Sheikh Aminu Daurawa

LADUBBAN DA AKE BI ALLAH ﷻ YA AMSA ADDU’A

Akwai ladubba da ake neman duk mai son Allah ﷻ ya amsa masa addu’arsa ya gabatar da su a ya yin addu'ar da gabaninta da kuma bayanta. Su ne:

1- Ana son mai addu'a ya fuskanci Allah ﷻ da kyakykyawar niyyah mai tsarki, ya sakankance cewa Allah ﷻ ne kaɗai zai iya biya masa wannan buƙatun nasa shi kaɗai, don haka wajibi ne ya halarto faɗin Allah ﷻ inda yake cewa:)

Ma’ana:

“Ku roƙi Allah ﷻ Ubangijinku kuna masu ƙanƙan da kai da bayyanar da tsoron Allah ﷻ da karyewar zuciya da mai da al'amari zuwa gare Shi a cikin zuciya, domin Allah ﷻ baya son masu ta’adɗanci da ƙetare iyaka.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan PDP, Gwamna Wike Ya Yi Sabuwar Tafiya

An karɓo daga Mua'zu Ɗan Jabal ya ce, ya yin da Ma’aiki ﷺ ya aike ni ƙasar yaman sai nace da shi, ka yi min wasiyya ya Ma’aikin Allah ﷺ, sai ya ce,

Ma’ana:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ka tsarkake ibadarka ka nufaci Allah ﷻ da ita, idan ka yi haka aiki kaɗan sai ya wadatar da kai a wajen Allah ﷻ

2- Ya fara yabo da kirari ga Allah ﷻ, sai salati ga Annabi ﷺ saboda hadisin Fudhalata Bn Ubaid inda yake cewa, wata rana Manzon Allah ﷺ yana zaune sai wani mutum ya shigo ya yi sallah, da ya gama sallar sai ya fara addu’a kai tsaye yana cewa, ya Allah ﷻ ka yi min gafara ka yi min rahma, sai Ma’aiki ﷺ ya ce da shi, ))

Kara karanta wannan

2023: Karin Matsala Ga Atiku, Jigon PDP Da Ɗaruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Ma’ana:

“Ya kai mai wannan sallah ka gaggauta wannan addu’ar taka, (yadda ba za a karɓe ta ba) idan ka yi sallah (sai ka nufaci yin addu'a), idan ka zauna sai ka godewa Allah ﷻ ka yi masa kirari da irin abin da ya cancance shi, sannan ka yi salati a gare ni, sannan sai ka roƙi Allah ﷻ abin da kake so. To bayan wannan lokacin kuma sai wani mutum ya yi sallah ya tsuguna zai yi addu’a, sai ya yi yabo ga Allah ﷻ ya yi kirari a gare shi, sannan ya yi salati ga Annabi ﷺ sai Ma’aiki ﷺ ya ce, ya kai wannan mai sallah roƙi Allah ﷻ za a amsa maka.”

3- Mutum ya yi addu’a yana mai sakankancewa, cewa Allah ﷻ zai karɓa masa, saboda hadisin Abu Hurairah inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce :

Ma’ana:

“Ku roƙi Allah ﷻ kuna masu yaƙini da sakankancewa za a karɓa muku, ku sani cewa Allah ﷻ baya karɓar addu’a daga gafalalliyar zuciya rafkananniyya mai wasa.” wannan hadisin mai kyau ne.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa a PDP: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Yace Yana Nan Tare da Gwamna Wike

4- Ana son mai addu’a ya yi nacin roƙon abin da yake son Allah ﷻ ya ba shi, saboda hadisin da yake cewa, “Lallai Allah ﷻ yana son masu na ci da dagewa a cikin addu’arsu.”

5- Ya halarto da zuciyarsa ga Allah ﷻ a lokacin da yake addu’ar, kada ya bari wani abu ya ɗauke hankalinsa ga barin jin Allah ﷻ

a cikin zuciyarsa a lokacin da yake cikin addu’a, saboda hadisi Abu Huraira wanda ya gabata kaɗan inda Ma’aiki ﷺ yake cewa:

Ma’ana:

“Lallai ku sani cewa, Allah ﷻ ba ya amsa addu’a daga zuciyar wanda ya gafala rafkanne mai wasa.”

6- Ya riƙa yin addu’a a lokacin tsanani da lokacin yalwa, kada yaƙi yin addu’a sai lokacin tsanani kawai , kamar yadda hadisi ya zo a kan hakan.

7- Kada mutum ya roƙi kowa sai Allah ﷻ, kamar yadda Ma’aiki ﷺ yake faɗa a hadisin Abdullahi Ɗan Abbas inda yake cewa,

Kara karanta wannan

Wani Azababben Yaƙi Ya Kaure Tsakanin Bello Turji da Tawagar Ƙasurgumin Ɗan Binidiga, Ɗan Bokolo

Ma’ana:

“Idan za ka yi roƙo ka roƙi Allah ﷻ, idan kuma za ka nemi taimako ka nemi taimakon Allah ﷻ...” Ka karanta hadisin har ƙarshensa.

8- Kada mutum ya yiwa kansa mummunar addu’a, ko ya yiwa ‘ya’yansa, ko kuma dukiyarsa, kamar yadda hadisin Ummu Salma ya nuna

. 9- Kada mutum ya riƙa daga murya sama-sama a ya yin addu’a, domin wanda kake kira ɗin ba kurma ba ne, ba kuma bebe ba ne. Kamar yadda Abu Musal Ash’ari yake cewa, mun dawo daga wani yaƙi tare da Ma’aiki ﷺ sai waɗansun mu suka hango garin Madina sai suka ɗaga muryoyinsu sama-sama suna yin kabbara sai Ma’aiki ﷺ ya ce, ( Ma’ana” “Lallai haƙiƙa Allah ﷻ Ubangijinku ba kurma ba ne, ba kuma a nesa yake ba, yana ji kuma yana nan a kusa da ku.

10- Mutum ya yarda da zunubinsa, ya nemi gafarar Allah ﷻ kuma ya san akwai ni’imar Allah ﷻ a kansa ya yi masa godiya.

Kara karanta wannan

Tsohon SGF a Mulkin Buhari da Wani Jigon APC Sun Sha Alwashin Yakar Tinubu/Shettima a 2023

11- Kada mutum ya kallafawa kansa gwanintar harshe a wajen addu’a, ma’ana ya ce dole sai ya yi addu'a da labari. Ko da ƙafiya.

12- Ya riƙa maimaita addu’a sau uku a lokaci ɗaya, wato idan ya faɗi buƙatarsa ya sake maimaita ta kamar yadda hadisi ya yi bayanin hakan.

13- Ya fuskanci Alƙibla idan zai yi addu’ar.

14- Ya daga hannayensa sama a ya yin wasu addu’o’i kamar yadda Anas Bn Malik yake cewa, )) Ma’ana: “Na ga Manzon Allah ﷺ yana ɗaga hannayensa biyu a ya yin addu’arsa.”

15- Ya yi alwala kafin ya shiga addu’ar.

16- Kada mutum ya wuce gona da iri a ya yin addu'ar tasa, kamar yadda hadisi ya yi hani akan hakan.

17- Mutum ya fara yi wakansa addu’ar, wato idan addua'r za ta haɗa da waninsa, saboda hadisin Ubayyu Ɗan Ka’abu inda yake cewa,

Kara karanta wannan

Karin Bayani: ASUU Ta Maida Martani Kan Hukuncin Kotu Na Janye Yajin Aiki

Ma’ana:

“Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya tuna wani, kuma yana son ya yi masa addu’a, sai ya fara yiwa kansa addu’ar, sannan sai ya yiwa wancan ɗin daga baya.” a wasu lokuta.

18- Ya yi tawassuli, ya yi kamun ƙafa da sunayen Allah ﷻ ko sifofinsa, ko da ƙaunarsa da yake yiwa Annabi ﷺ ko da salatin Annabi ﷺ ko kuma da wasu kyawawan ayyukan da ya yi don Allah ﷻ, kamar yadda wasu hadisai suka nuna hakan.

19- Ya kyautata abincinsa da abin shansa, ma'ana, abincinsa da abin shansa, su zamo na halal ne, kamar yadda hadisai suka nuna.

20- Kada mutum ya yi addu'a ta saɓo ko ta yanke zumunta kamar yadda hadisi ya gabata, a kan hakan.

21- Mutum ya riƙa yin umarani da kyakykyawan aiki ya riƙa hani da mummuna. 22- Mutum ya nisanci dukkanin saɓo karami da babba.

Kara karanta wannan

Akwai Wasu Mutane Dake Yi Wa Shugaba Buhari Zagon Ƙasa, Gwamna Yahaya Bello

23- Ana so a yi addu'a a daren lailatil ƙadri, domin dare ne na amsa addu'a.

24- Tsakiyar dare ana amsa addu'a kamar yadda hadisi ya nuna hakan.

25- Ana amsa addu'a a tsakanin kiran sallah da tayar da iƙama, kamar yadda hadisi ya nuna hakan.

26- Ana amsa addu'a a kowanne lokaci da daddare.

27- Ana amsa addu'a a ƙarshen kiran kowacce sallah ta farilla.

28- Ana amsa addu'a ya yin saukar ruwan sama, kamar yadda hadisai suka nuna hakan. 29- Ana amsa addu'a a lokacin da aka yi sahu-sahu za a tafi yaƙin ɗaukaka kalmar allah ﷻ da kuma ya yin da aka yi sahun kafin a fara yaƙin, kamar yadda hadisai suka nuna hakan. 30- Ana amsa adu'a a ranar juma'a a wani lokaci musamman ma bayan sallar juma'ar zuwa faɗuwar rana. Musamman bayan la'asar.

31- Ana amsa addu'a ya yin da za a sha ruwan zamzam tare da kyakykyawar niyyah, kamar yadda hadisi ya nuna.

Kara karanta wannan

2023: Dole Mu Tabbatar da Najeriya Gabanin Shugaban Kasa, Jonathan

32- Ana amsa addu'a a cikin sujjada, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.

33- Idan mutum ya farka da daddare ya yi irin addu'ar da Ma’aiki ﷺ yake yi da daddare, za a amsa masa addu'arsa.

34- Ana amsa addu'ar wanda ya kwaikwayi irin addu'ar da Annabi ﷺ Yunusa ya yi, it ace: “La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin.”

35- Ana amsa addu'a a cikin tahiyyar sallah ta ƙarshe, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.

36- Idan Musulmi ya yiwa ɗan uwansa Musulmi addu'a ba tare da ya sani ba, ita ma karɓaɓɓiyar addu'a ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.

37- Addu'ar ranar arfa ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan. 38- Idan musulmai suka haɗu wasu suna addu'a wasu suna cewa amin, ita ma wannan addu'ar karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.

Kara karanta wannan

Kano 2023: Abba Gida Gida Ya Magantu Kan Wani Faifan Bidiyo da Aka Jingina Masa

39- Ana amsa addu'a a ya yin da mutum ya fuskanci Allah ﷻ da tsarkin zuciya, wato iklasi mai ƙarfi.

40- Addu'ar wanda aka zalunta a kan wanda ya zalunce shi, ita ma karɓanniya ce, kamar yadda ya tabbata a adisin Mu’az

41- Addu'ar mahaifi ko mahaifiya ga ɗansu, ita ma karɓaɓɓiya ce nan take, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.

42- Addu'ar matafiyi a halin tafiya, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.

43- Addu'ar mai azumi a lokacin buɗa baki, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar.

44- Addu'ar wanda ya shiga cikin matsananciyar buƙata, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar aya da hadisi suka tabbatar da hakan.

45- Addu'ar shugaba adali, ita ma karɓaɓɓiya ce.

46- Addu'ar ɗa na kirki ga iyayensa, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Kai Sabon Harin Bama-Bamai Maɓoyar Bello Turji a Zamfara

47- Addu'a bayan an gama alwala, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yadda hadisi ya yi bayani a kan hakan.

48- Yin addu'a bayan an gama jifan sheɗan, na ɗaya da na biyu, ita ma karɓaɓɓiya ce, kamar yada hadisi ya kawo.

49- Yin addu'a a cikin Ka'aba idan an sami damar shiga cikinta da kuma yin addu'a a cikin hijir-Isma'il, wato wannan ɗan kewayen da yake a jikin ɗakin Ka'aba, karɓaɓɓiya ce.

50- Yin addu'a a kan dutsen safa, ita ma karɓaɓɓiya ce.

51- Yin addu'a akan dutsen marwa, ita ma karɓaɓɓiya ce.

52- Yin addu'a a mash'aril haram, wato a muzdalifa, ita ma karɓaɓɓiya ce.

Allah ya karɓi addu'o'in mu.

ZA mu ci gaba insha Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel