Kano: Miji da Mata Sun Sace Yarinya ’Yar Shekara 17, An Gano Matakin da Kotu Ta Dauka

Kano: Miji da Mata Sun Sace Yarinya ’Yar Shekara 17, An Gano Matakin da Kotu Ta Dauka

  • Wata kotun majistire da ke jihar Kano ta garkame wasu ma'aurata bisa tuhumarsu da laifin garkuwa da wata 'yar shekara 17
  • A yayin da aka shigar da su kara, ma'auratan su ma sun shigar da wata karar gaban babbar kotu don hana a kulle su
  • Sai dai alkalin kotun majistiren ya ce shari'o'in biyu sun bambanta, kuma barinsu a gida hatsari ne, don haka ya sa a kulle su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - An gurfanar da wasu ma’aurata Mista & Misis Matthew Auta mazauna karamar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano a gaban wata kotun majistare da ke Nomansland.

An gurfanar da miji da matar ne bisa laifin hada baki da sace wata yarinya ‘yar shekara 17 mai suna Amira Isah Takai.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

Kotu ta garkame miji da mata a Kano
Kano: Kotu ta dauki mataki kan ma'auratan da ake zargin sun sace yarinya 'yar shekara 17. Hoto: Federal High Court
Asali: UGC

Wadanda ake tuhumar sun shigar da wata kara babbar kotu

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun musanta tuhumar da ake yi musu a lokacin da mai gabatar da kara, Insifekta Fago Lale ya karanta karar su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan wadanda ake kara ya roki kotun da ta bada belin su saboda sun shigar da kara a gaban wata babbar kotun Kano karkashin jagorancin Mai shari'a Aisha Mahmud.

Sun shigar da karar ne suna neman a dakatar da kwamishinan ‘yan sanda da jami’in ‘yan sanda na Tudun Wada daga tauye hakkinsu na 'yan Adam.

Hukuncin da kotun majistire ta yanke kan ma'auratan

Sai dai alkalin kotun, Ibrahim Mansur Yola, ya bayyana cewa shari’o’in biyu sun banbanta domin daya na neman hakkin bil’adama ne, dayan kuma yana kan laifin da ake zargin sun aikata.

Kara karanta wannan

Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Alkalin kotun ya bayyana cewa zamansu a gidan yari ya fi zamansu a gida alfanu, kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Janairu.

A Kano din ne kuma aka taba sace wata yarinyar 'yar shekara 17, diyar wani dan majalisar jihar bayan da 'yan bindigar suka so sace mahaifin, kamar yadda Tribune online ta ruwaito.

Ekiti: Yan daba sun sace wata gawa a asibitin EKSUTH

A wani labarin, 'yan daba sun kutsa cikin asibitin koyarwa na jami'ar Ekiti, inda suka sace gawar wani mutum jim kaDan bayan mutuwarsa.

An ruwaito cewa 'yan dan sun ci zarafin ma'aikatan asibitin tare da lalata wasu kayayyaki a sashen hadurra da ba da agajin gaggawa kafin suka sace gawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel