FG Ta Saki Sunayen Kamfanonin Najeriya da Suka Cancanta Su Nemi Kwangilar Gwamnati a 2024

FG Ta Saki Sunayen Kamfanonin Najeriya da Suka Cancanta Su Nemi Kwangilar Gwamnati a 2024

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen kamfanonin da suka cancanci neman kwangila daga wajen gwamnati
  • Jerin sunayen, wanda ya hada da kamfanoni sama da 1,000, ya shafi sassa daban-daban na ayyukan raya tattalin arzikin Najeriya
  • Kamfanonin da aka zabo sun bi dokar fansho ta Najeriya kafin gwamnatin tarayya ta ba su damar neman kwangilar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Hukumar fansho ta kasa (PENCOM) ta bayyana cewa kamfanoni 1,081 ne suka samu takardar shaidar biyan ma'aikata fansho.

Tare da wadannan takaddun shaidar biyan fansho, kamfanonin bisa doka, yanzu sun cancanci neman kwangilar gwamnati a shekarar 2024.

Jerin kamfanonin da gwamnati za ta ba kwangila a 2024
FG ta saki sunayen kamfanonin Najeriya da suka cancanta su nemi kwangilar gwamnati a 2024. Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Jerin, wanda aka buga a ranar 4 ga Janairu, 2024, a shafin yanar gizon PENCOM, ana sa ran za a ci gaba da sabunta shi har zuwa karshen shekarar.

Kara karanta wannan

Tsageru sun farmaki motar kamfen mataimakin gwamnan PDP, sun tafka mummunar ɓarna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayyar Najeriya da kananan hukumomi 36 na kasar za su kashe naira tiriliyan 44.94 domin gudanar da ayyuka na yau da kullum da kuma manyan ayyuka a shekarar 2024.

Abubuwan da ake bukata don samun kwangilar gwamnatin tarayya

Dangane da ka'idojin dokar fansho na kasa, dole ne kamfani ya wuce mafi karancin bukatun bude asusun fansho da inshorar rai ga kamfani don samun takardar shaida daga hukumar.

Dokar ta bayyana cewa kamfanonin da ba su da inshora ga ma'aikatansu ba za a ba su damar yin kasuwanci da gwamnati ba.

PenCom ta yi imanin cewa idan aka bi wannan ka'idar, kamfanonin za su tabbatar da cewa akwai asusun fansho masu ga ma'aikatan su.

Jerin kamfanonin da aka amince da su don ayyuka a 2024

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

  • Spectrum Engineering Limited
  • Logarithm Energy Limited
  • Straightforth Energy Solutions Limited
  • Mercantile Int'l Wheels Limited
  • Allworth Engineering Limited
  • Satimaiha Nigeria Limited
  • Stargro Nigeria Limited
  • Diamond Fcy Ltd
  • Atomic Diamond Limited
  • Hesaab Engineers And Consultants Limited
  • Dalori Global Engineering Limited
  • Von Engineering Limited
  • Great Lakes Engineering Limited
  • Hikam Engineering And Consultancy Limited
  • Grandworth Nigeria Limited
  • Florish Engineering Limited
  • Jafi Security Limited
  • Wumech Engineering Services Ltd
  • Malfatash Ventures Limited
  • Merak Meraki Global Consults Limited
  • Wan Diyos Limited
  • Fachartz Consulting Ltd
  • Asss Engineering Ltd
  • Waren Bao Limited
  • Dexterity Developments Limited
  • Konstrad Nigeria Limited

Ana iya shiga nan domin sauke cikakken jerin kamfanoni 1,081.

Jerin kanfanonin da za su yi dillancin man Dangote

A wani labarin kuma, kamfanoni bakwai sun kammala rijista da matatar mai ta Dangote domin fara dillancin man fetur a Najeriya.

Legit Hausa ta tattaro jerin sunayen kamfanonin wadanda a kowanne lokaci za su iya fara siyar da man.

Asali: Legit.ng

Online view pixel