Kano: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dan Daba da Ya Kashe Limami, Ta Kuma Hada da Mahaifinsa
- Mai shari'a Binta Ibrahim-Galadanchi ta kotun majistire, ta ba da umurnin garkame matashin da ya kashe limami a Kano
- An gurfanar da Yusuf Haruna kan zargin ya daba wa Liman Sani Mohammed wuka har lahira a watan Disamba 2023
- Haka zalika, Mai shari'a Ibrahim-Galadanchi ta garkame mahaifin Yusuf saboda zarginsa da boye dansa bayan kashe limamin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Wata kotun majistare da ke Kano, a ranar Laraba, ta garkame matashi dan shekara 18, Yusuf Haruna, a gidan yari, bisa zarginsa da kashe wani limami mai suna Sani Mohammed ta hanyar daba masa.
Wanda ake karar mazaunin unguwar Tudun Nufawa da ke Kano, ana tuhumarsa da laifin kisan kai.
Mai gabatar da kara, Misis Fatima Ado-Ahmad, ta shaida wa kotun cewa wani Musa Yunusa ne ya kai rahoton kisan ga ofishin ‘yan sanda na Jakara, Kano a ranar 31 ga Disamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Haruna ya ki amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa
Daily Trust ta ruwaito cewa jami'ar ta yi ikirarin cewa misalin karfe 7:00 na dare Haruna ya dabawa limamin wuka mai kaifi a bayansa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanya aikata wannan laifin da ake zarginsa da shi.
Alkaliyar kotun, Mai shari’a Binta Ibrahim-Galadanchi, ta bayar da umarnin a garkame wanda ake kara a wani gidan gyaran hali da ke Kano.
Sannan ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 31 ga watan Janairu domin samun karin bayanai, Daily Post Nigeria ta ruwaito.
Kotu ta garkame mahaifin Yusuf da ya kashe Liman Sani
A wani labarin kuma, mahaifin Yusuf “Haruna Sani” ya gurfana a gaban kotun majistare saboda boye dansa bisa zargin kashe Liman Sani Mohammed.
Jami'in da ya shigar da karar, Ado-Ahmad, ya ce a ranar 31 ga Disamba, 2023 wanda ake kara ya boye dansa “Yusuf” bayan ya daba wa Mohammed wuka har lahira.
Alkaliyar kotun Binta Ibrahim-Galadanchi, ta bayar da umarnin a garkame wanda ake kara a gidan gyaran hali.
Dan daba ya caka wa limami wuka saboda ya hana su shan wiwi
A ranar Alhamis ne Legit Hausa ta ruwaito maku cewa 'yan sanda sun kama wani dan daba da ya caka wa lami wuka har lahira a Kano saboda ya hana su shan wiwi a kusa da masallaci.
Rahotanni sun bayyana cewa Yusuf Haruna da aka fi sani da Lagwatsani ya kashe Liman Sani Mohammed a ranar 31 ga watan Disambar 2023 a unguwar Jakara da ke Kano.
Asali: Legit.ng