'Yan bindiga sun harbe wani limami a Kaduna saboda yawan sukarsu a hudubarsa
- 'Yan bindiga a jihar Kaduna sun kashe babban limamin kauyen Kwaran Rafi a karamar hukumar Igabi
- Muryar marigayi, babban limanmin kauyen, Danleeman Isah, ta yi fice wajen suka da Alla-wadai da ayyukan 'yan bindiga
- Kazalika, wasu 'yan bindigar sun kashe sarkin yakin Godogodo da wasu sauran mutane a Jema'a da Kajuru
A wasu hare-hare daban-daban guda biyu da 'yan bindiga suka kai a kananan hukumomi biyu da ke jihar Kaduna, sun kashe limamin wani Masallaci da karin wani mutum guda, kamar yadda Punch ta rawaito.
Kamishinan tsaron cikin gidan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyen Kwaran Rafi a karamar hukumar Igabi tare da kashe babban limamin Masallacin kauyen, Danleeman Isah.
Aruwan ya sanar da cewa; "kai tsaye 'yan bindigar suka dira gidan Isah inda suka harbe shi tare da barin gidan ba tare da daukan komai ba, sun je gidan ne domin kawai su kashe shi.
"Ba za'a rasa nasaba tsakanin kisan Limamin da yawan sukar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a hudubarsa ba.
KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su
"Kazalika, a cikin watan Oktoba, 2020, 'yan bindiga sun sake kashe wani mutum, Ardo Musa Layi, a karamar hukumar Kajuru bayan sun sace shi saboda yawan suka da adawarsa da kisan mutane, garkuwa da mutane, da satar shanu.
"A wani salo kwatankwacin irin hakan, wasu 'yan bindigar sun harbi wani mutum, Ardo Ahmadu Suleiman, a Kasuwar Magani, karamar hukumar Kajuru, inda suka bar shi da raunukan harsashi."
Kwamishinan ya kara da cewa jami'an tsaro a jihar Kaduna sun sanar da mutuwar Sarkin Yakin Godogodo, Mista Yohanna Abu, wanda gungun 'yan ta'adda suka kashe.
KARANTA: Kano: 'Yan sanda sun kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da karasa (Bidiyo)
Ya kara da cewa 'yan bindigar sun kai hari kauyen Nisama a karamar hukumar Jema'a a daren ranar Juma'a inda suka sace Abu da wani mazaunin kauyen mai suna Mista Charles Audu.
"Mutanen biyu sun yi kokarin tserewa daga hannun 'yan bindigar, yayin da Audu ya samu damar tsira, 'yan bindigar sun harbe Audu," a cewar Aruwa.
Aruwan ya bayyana cewar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya bayyana damuwarsa akan kisan tare da yin addu'ar Allah ya jikan mamatan.
A kwankin baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta kara daukar mataki na gaba bayan sanar da rufe makarantu da wuraren taron biki da gidajen rawa.
A wani sako da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar ya sanar da cewa ma'aikata kasa da mataki na 14 su cigaba da zama a gida a yayin da aka bayar da sabbib ka'idoji ga Masallatai da Coci.
Kaduna na daga cikin jihohin da ake ake samun hauhawar alkaluman masu kamuwa da korona a kowacce rana a 'yan kwanakin baya bayan nan.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng