Matar da Ta Sha Suka Saboda Tashin Asuba Don Girkawa Mijinta Abinci Ta Samu Sama da N2m

Matar da Ta Sha Suka Saboda Tashin Asuba Don Girkawa Mijinta Abinci Ta Samu Sama da N2m

  • Ganin mutunci da nuna soyayyar da wata yar Najeriya ta yi wa mijinta ya amfaneta yayin da yan Najeriya suka ci gaba da tura mata kudi
  • Zuwa yanzu, ta samu kudi sama da naira miliyan 2 a asusunta, firinji da kuma tayin aiki nata da na mijinta
  • Matar da ta cika da mamaki ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin yi wa jama'a godiyar kudin da suka tura mata bayan ta sha caccaka saboda tashin asuba don yi wa mijinta girki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A wani yunkuri na nuna mata goyon baya, yan Najeriya sun turawa wata mata da ta sha suka a soshiyal midiya bayan ta bayyana yadda take tashi da karfe 4:40 na asuba don girkawa mijinta abinci, kyautar kudi sama da naira miliyan 2.

Kara karanta wannan

Matashi ya ba budurwarsa ta shekaru 7 naira miliyan 5 don ta bari ya auri wata daban, ta yi martani

Awanni bayan ta baje kolin kudi fiye da naira miliyan 1 da mutane suka aika mata, matar mai suna @_Debbie_OA, ta koka cewa ya kai sama da naira miliyan 2.

Mutane sun tura mata kyautar kudi
Matar da ta sha suka saboda tashin asuba don girkawa mijinta abinci ta samu sama da N2m Hoto: @_Debbie_OA
Asali: Twitter

Ta nuna yawan kudin da ke cikin asusunta na banki yayin da ta yi godiya ga jama'a kan wannan soyayya da goyon baya da suka nuna mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina rubutun da ke dauke da lambar ajiya na bankina ma ne wai. Don Allah ya isa haka, na tsorata," ta rubuta.

@_Debbie_OA ta kuma sanar da cewar wata yar kasuwa ta yi mata kyautar firinji. Bincike kan shafinta ya kuma nuna an bata wani aiki da za a biya N50k.

Mutane sun yi wa mijinta tayin aiki.

Ga wallafar tata a kasa:

Jama'a sun yi martani

@iam_Bjlee ya ce:

"Sannan wasu mutane na ta kuka saboda tana tashi da karfe 4:50 na asuba don girkawa wanda take so abinci."

Kara karanta wannan

An tara wa matar aure naira miliyan daya cikin awanni sanadin tashi da asuba ta yi wa mijinta girki

@47kasz ya ce:

"Wannan ma ban da katifa, firinji, abun nika, abun dumama abinci da sauransu da ta samu!!! Kin cancanta ba wai don kin rubuta bane i;;a saboda ganin mutunci da girman mijinki ne."

@RealAdeshina ya ce:

"Yanzu zan iya bacci. Manufarmu ita ce 2m kuma ga mu nan.
"Godiya ga kowa da kowa.
"Allah ya albarkaci iyalinku.
"Mazan twitter 100-0 mata masu ganin kansu na twitter."

Kotu ta bada umurnin kamo wani kwastam

A wani labari na daban, mun ji cewa kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta bayar da umarnin kama wani jami'in kwatsam mai suna Yusuf Ismail Mai Biscuit, bisa kin amsa sammacin da aka tura masa.

Alkalin kotun, Garba Malafa ne ya bayar da umurnin bayan rokon da lauyan mai kara, Idris Saleh Bello ya yi, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel