“Sun Kama Kansu”: Matashi Ya Yi Arba da Yan Mata 18 da Suka Yi Soyayya a Wajen Bikinsa

“Sun Kama Kansu”: Matashi Ya Yi Arba da Yan Mata 18 da Suka Yi Soyayya a Wajen Bikinsa

  • Wasu yan mata 18 da suka sha soyayya da wani matashi sun isa wajen bikinsa domin shaida daurin aurensa
  • A wani abu mai kama da shiri na musamman, an ce gaba daya yan matan sun kama kansu a wajen bikin
  • An ce sun ci sun sha sannan suka taka rawa cikin kwanciyar hankali ba tare da tayar da hankalin amarya da ango ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jama'a sun yi martani kan labarin wasu yan mata 18 da suka isa wajen bikin mutumin da ya yi soyayya da su a baya.

A wani abin da ya yi kama da shirin nuna hadin kai, yan matan sun yi dirar mikiya a wajen daurin auren inda suka shiga sahun sauran mahalarta biki domin yi wa tsohon saurayin nasu fatan alkhairi.

Kara karanta wannan

Budurwa ta koka yayin da saurayi ya yasar da ita a filin jirgin sama, tana neman taimako

Yan mata sun halarci daurin auren tsohon saurayinsu
An yi amfani da hoton don misali ne mutanen basu da alaka da labarin Hoto: Getty Images/Jose Luis Pelaez Inc and Mint Images.
Asali: Getty Images

A cewar labarin wanda Wizarab ya bayar a dandalin X, an ce yan matan sun nuna halin dattako a iya zamansu a wajen taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abun da suka yi da suka isa wajen bikin

Wizarab ya ce sun kama kansu, suka yi rawa da cin abiunci kamar kowa sannan ba su kowa ciwon kai ba.

Labarin ya ce:

"A wajen bikin gayen nan, sama da yan mata 18 da ya kwana da su sun hallara. Magana ta gaskiya abokansa sun daina kirga su a lokacin da suka kai 18 sannan suka fara dariya. Babu wacce ta nuna karanta. Sun kama kansu, suka ci abinci da rawa don godiya ga Allah."

Kalli labarin a kasa:

Jama'a sun yi martani

@InalegwuSZN ta tambaya:

"18 kuma babu wacce ta nuna halin 'karanta kamar yaya?"

@Bady4christ ya ce:

Kara karanta wannan

Kotun koli na shirin yanke hukunci, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake motsi mai girma a jihar Kano

"Lallai amma dai gayen na da kudi."

@Jidekuje ya ce:

"Na tabbata wasu daga cikin gayun da suka kwanta da matashiyar ma suna a wajen. Kuma za su kama kansu kamar kodayaushe. Yana yadda yake."

@gagnanttt ya ce:

"Lallai gayen nan jarumi ne."

Budurwa ta koka kan saurayi

A wani labarin, mun ji cewa wata budurwa ƴar Najeriya ta shiga damuwa bayan ta gano cewa saurayin da ta daɗe tana yi wa jan aji ya auri wata daban.

An nuna budurwar cikin wani bidiyo tana ta kuka kan lamarin bayan ta gano cewa saurayin ya yi auren shi ya fita harkarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel