Ziyarar Dan Sarkin Kano Zuwa Coci: Hadimin Sarkin Benin Ya Yi Karin Haske

Ziyarar Dan Sarkin Kano Zuwa Coci: Hadimin Sarkin Benin Ya Yi Karin Haske

  • Masarautar Benin ta yi karin haske kan ziyarar da dan sarkin Kano ya kai babbar cocin Benin don taya Sarki Ewuare II murnar sabuwar shekara
  • An samu rudani a sanarwar da masarautar ta fitar a ranar 31 ga watan Disamba 2023, inda ta ce Yarima Isah dan sarkin kano Aminu Ado-Bayero ne
  • Sai dai a sabuwar sanarwar da da fitar ranar Laraba, ta yi karin haske kan dan sarkin Kanon da ya ziyarce su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Benin, jihar Edo - Sarkin Benin Uku Akpolokpolo, Ewuare II, ta bakin sakataren watsa labaransa, Osaigbovo Iguobaro ya yi karin haske kan ziyarar dan sarkin Kano zuwa coci.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa ya kamata Atiku ya hakura da takarar shugaban kasa, Deji Adeyanju

Idan ba a manta ba, a ranar 31 ga watan Disamba, rahotanni suka bayyana cewa dan sarkin Kano, Isah Ado-Bayero, ya yi wa sarkin Benin kara a bikin maraba da sabuwar shekara.

Gaskiya game da dan sarkin gano da ya kai ziyara cocin Benin
Masarautar Benin ta yi karin haske kan dan sarkin Kano da ya kai ziyara coci. Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Abin da ya faru a ranar Litinin da data gabata

Iguabaro ya ce Yarima Isah dan sarki marigayi, Alhaji Ado Bayero ne, ba dan sarkin Kano na yanzu Alhaji Aminu Ado-Bayero ba, kamar yadda aka ruwaito a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sakatare watsa labaran a wata sanarwar a ranar Litinin da ta gabata ya ce:

"Majami'ar Holy Aruosa Cathedral ta yi babban bako, Yarima Isa Ado Bayer, dan sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero.
"Wannan ziyar ta kayatar da masu bauta a majami'ar, kuma hakan na nuna dattakun da ke tsakanin masarautar Kano da kyakkyawar alakarsu da al'ummar Kirista."

Kara karanta wannan

'Dan Sarkin Kano ya bada mamaki, ya haɗu da fitaccen sarki a Najeriya sun je coci taron addu'o'i

Masarautar Benin ta warware rudanin da aka samu

Daily Trust ta tuntubi masautar biyo bayan fitar sanarwar don tabbatarwa, inda ta gano Yarima Isah ba dan sarkin Kano na yanzu ba ne.

Da ya ke magana da jaridar a ranar Laraba, Iguobaro ya yi karin haske kan cewa Yarima Isah da ne ga marigayi sarkin Kano.

Ya ce:

"An gabatar mana da shi matsayin dan sarkin Kano ba tare da an bambance mana ko dan sarkin yanzu ko na marigayi ba ne."

Dan sarkin Kano ya je coci taron addu'o'i tare da sarkin Benin

A makamancin labarin da Legit ta wallafa a ranar Litinin, Sarkin Benin, Oba Ewure II ya karbi bakuncin Yarima Isah Ado-Bayero, dan Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero.

A ziyarar ne yariman ya bi sahun sarkin Benin, inda suka je babbar majami'ar Benin don halartar taron addu'o'i na murnar shiga sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel