Yan Bindiga Sun Halaka Abokan Juna a Wani Sabon Hari a Jihar Nasarawa

Yan Bindiga Sun Halaka Abokan Juna a Wani Sabon Hari a Jihar Nasarawa

  • An shiga jimami bayan ƴan bindiga sun halaka wasu mutum biyu a wani sabon hari da suka kai a jihar Nasarawa
  • Ƴan bindigan sun halaka mutanen a ƙauyen Wulko dake ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa
  • Jami'an ƴan sandan jihar Nasarawa sun kuma samu nasarar ceto wani malamin jami'a da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Wasu ƴan bindiga sun kashe mutum biyu a ƙauyen Wulko da ke ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa.

Mutanen da aka kashen sun haɗa da Ango Habakkuk, wanda aka fi sani da (Ango Gentle), da Ewuga Williams, wani jami’in tsaro, wadanda manyan abokai ne kuma mazauna ƙauyen Wulko, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tafka sabon ta'adi, sun halaka bayin Allah da sace gomman mutane

Yan bindiga sun halaka abokai biyu a Nasarawa
Yan bindiga sun halaka abokan juna a Nasarawa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa an binne Williams kamar yadda addinin Kirista ya tanada, yayin da aka ajiye gawar Habbakuk a ɗakin ajiye gawa na asibitin Ola da ke Akwanga a jihar Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun ceto malamin jami'a

A halin da ake ciki, rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa tare da haɗin gwiwar ƴan banga sun ceto wani malamin jami'a mai suna Mista Isaac Igbawua, malami a sashen Micro Biology na jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi.

Rundunar ta kuma kama wani ɗalibi mai shekar 25 ɗan 200L na sashen Social Works a jami'ar tarayya dake Lafia, Favor Chukwuebuka bisa zargin mallakar bindiga.

A cewar rundunar yan sandan, kayayyakin da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun haɗa da bindigar Beretta ta gida guda ɗaya da kuma harsashi mai rai guda huɗu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Rahman Nansel, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana tuni aka haɗa malamin jami'an tare da iyalansa.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan a yayin harin sun bindige mutum uku har lahira tare da yin awon gaba da Hakimin wani ƙauye a yayin harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel