Harin Plateau: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Laifin Tinubu, Ta Gaya Masa Muhimmin Abu 1 da Ya Kamata Ya Yi

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Laifin Tinubu, Ta Gaya Masa Muhimmin Abu 1 da Ya Kamata Ya Yi

  • Jam'iyyar PDP ta yi magana kan matakin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kamata ya ɗauka kan harin Plateau
  • Jam'iyyar adawar ta buƙaci shugaban ƙasan da ya ziyarci mutanen da harin ya ritsa da su tare da tabbatar da an zaƙulo miyagun da suka kai harin
  • Mummunan harin dai wanda aka kai a ƙananan hukumomi biyu na jihar, ya laƙume rayukan sama da mutum 150

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Jam’iyyar PDP ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ziyarci wurin da wasu ƴan bindiga suka kashe ƴan Najeriya a jajibirin Kirsimeti a yankin Bokkos da Barkin Ladi na jihar Plateau.

Shugaban masu sa ido kan zaman lafiya na al’umma a ƙaramar hukumar Bokkos, jihar Plateau, Kefas Mallai, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kashe sama da mutum 150.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nuna alhini kan rasuwar Ghali Na'Abba, ya aike da sako mai muhimmanci

PDP ta shawarci Tinubu kan harin Plateau
PDP ta bukaci Tinubu ya ziyarci Plateau Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, ya yi Allah wadai da hare-haren tare da bayar da umarnin farautar waɗanda suka kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Filato, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa "waɗannan jakadun mutuwa, ciwo da baƙin ciki ba za su tsira daga shari’a ba."

PDP ta aike da saƙo ga Tinubu

Da yake mayar da martani, sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ya yi tambaya kan abin da ya jawo gazawar bayanan sirri kafin da kuma lokacin da aka kai harin.

A kalamansa:

"Abin damuwa shi ne, ƴan Najeriya su ma suna ta taɓo batutuwa a kan waɗannan fargaba ta hanyar yin la’akari da furucin da ake dangantawa da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, kan yiyuwar haɗa baki daga jami’an gwamnati wajen tayar da zaune tsaye ko kuma a tada ƙayar baya kamar irin yadda aka gani ya faru a Jihar Filato."

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaba Tinubu ya dira a jihar arewa bayan kashe bayin Allah sama da 100

Jam'iyyar adawar ta buƙaci Tinubu da ya kawar da shakku kan hakan, ta hanyar ziyartar al'ummar da abin ya shafa cikin gaggawa, sannan ya yi wa ƴan ƙasa cikakken jawabi kan ƙwararan matakan da za a ɗauƙa domin zaƙulo miyagun da masu ɗaukar nauyinsu.

Shetttima Ya Ziyarci Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ziyarci jihar Plateau sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai.

Mataimakin shugaban ƙasan ya ziyarci mutanen da suka yi gudun hijira daga matsugunansu a sakamakon harin na jajibirin Kirsimeti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel