Yan BindIga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Bayin Allah a Wani Yanayi Mara Dadi

Yan BindIga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Bayin Allah a Wani Yanayi Mara Dadi

  • An shiga jimami a jihar Sokoto bayan ƴan bindiga sun tafka ta'asa a wani mummunan hari da suka kai a jihar Sokoto
  • Miyagun ƴan bindigan a yayin harin sun ƙona wata mata da surukurarta da ƴaƴanta biyu a ƙaramsar hukumar Rabah
  • Ƴan bindigan sun kuma halaka wasu mutum 12 da sace wasu mata uku a harin da suka kai a daren ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Wasu miyagu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun ƙona wata mata da surukarta da kuma ƴaƴanta biyu da ransu a wani harin da suka kai a jihar Sokoto.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Kurya da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Ana cikin bikin Kirsimeti yan bindiga sun kai mummunan hari a jihar Arewa, sun halaka mutum 6

Yan bindiga sun halaka mutane a Sokoto
Yan bindiga sun salwantar da rayukan bayin Allah a Sokoto Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun kashe mutanen ƙauyen 12 tare da sace mata uku a yayin harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin, Yusuf Garba ya ce ɗaya daga cikin wadanda aka sace ta rasa mijinta a harin, rahoton Trust Radio ya tabbatar.

"Daga cikin wadanda aka kashe akwai wata mace ɗaya da aka ƙona ta mutu tare da surukarta da ƴaƴanta biyu a cikin ɗakinsu." A cewarsa.

A cewarsa, daga baya maharan sun yi wani ƙazamin faɗa da sojoji.

"Muna zargin su ma sun yi asara mai yawa saboda mun ga tabon jini a inda suka ajiye babura. Amma ka san ba sa barin gawarwakinsu a baya." A cewarsa.

Me ƴanda suka ce kan lamarin?

Sai dai rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai ne a yayin harin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka halaka babban likita a yanayi mara dadi a gaban iyalansa

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, ya ƙara da cewa suna cigaba da tattara alƙaluman waɗanda suka mutu.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Ƴan Kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan wasu ƴan kasuwa a jihar Katsina.

Ƴan bindigan a yayin farmakin sun halaka mutum shida har lahira tare da raunata wasu mutum huɗu tare da yin awon gaba da wasu mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel