Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Kwaleji a Jihar Arewa Bayan Karbar Naira Miliyan 2

Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Kwaleji a Jihar Arewa Bayan Karbar Naira Miliyan 2

  • Bayan makonni uku da yin garkuwa da shi tare da wasu da dama, 'yan bindiga sun kashe malamin kwalejin ilimi ta jihar Zamfara
  • Yan bindigar sun kashe Malam Nasiru Mohammed Anka bayan karbar kudin fansa har naira miliyan biyu daga iyalansa
  • Wata mata da 'yan bindigar suka kama amma ta samu nasarar kubutowa ta sanar da mutuwar malamin tare da fadin silar mutuwar ta shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Maru, jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun kashe Malam Nasiru Mohammed Anka, malami a kwalejin ilimi ta jihar Zamfara da ke Maru bayan karbar kudin fansa har naira miliyan biyu.

An yi garkuwa da marigayi Malam Mohammed ne a gidansa, wani rukunin gidajen gwamnati da ke kusa da kwalejin a Maru kimanin makonni uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Abin bai yi dadi ba: 'Yan bindiga sun mamaye wani gari a Zamfara, sun kashe mutane

Yan bindiga sun kashe malamin kwaleji a jihar Zamfara
Yan bindiga sun kashe Malam Mohammed Anka, malami a kwalejin Zamfara bayan karbar kudin fansa har naira miliyan biyu. Hoto: Nigeria Police
Asali: Facebook

Yadda 'yan bindiga suka sace Malam Mohammed a Maru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindigar sun yi garkuwa da shi ne tare da wasu mazauna unguwar lokacin da suka mamaye rukunin gidajen tare da daukar mutane da dama domin neman kudin fansa.

Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ‘yan bindiga suka mamaye garin Maru da ke tsakiyar hedikwatar karamar hukumar.

Wata majiya ta kusa da dangin malamin ta tabbatar wa TVC News faruwar lamarin.

Azabtar da Malam Mohammed da mutuwarsa

Majiyar ce ta ce wata mata da 'yan bindigar suka sace a wani lokaci daban da ta samu damar kubutowa daga hannunsu ta sanar da mutuwar malamin a sansanin barayin.

Ta ce an kashe shi ne a gabanta biyo bayan azabtarwar da masu garkuwar suka yi masa a sansaninsu bayan da iyalansa suka gaza biyan makudan kudaden da suka nema a matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

An shiga jimamin rashin manoma 4 da 'yan bindiga suka yiwa kisan gilla a jihar Katsina

Matar da ta yi karfin hali ta tserewa daga sansanin masu garkuwan ta kara da cewa kwana biyu da rasuwar malamin, barayin sun yi kokarin cire wasu sassa na jikinsa, amma saboda ya fara rubewa suka hakura suka bar shi.

Yan bindiga sun sace mawaki da masu masa amshi a hanyar Abuja

A wani labarin, kun karanta cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace wani mawaki Omoba De Jombo Beats da masu masa kida a hanyar Abuja zuwa Kogi.

Wani mawaki Boye Best ya wallafa labarin a shafinsa na Instagram inda ya ce 'yan bindigar suna neman naira miliyan 10 kudin fansar duk mutum daya

Asali: Legit.ng

Online view pixel