'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Abuja, Sun Sungume Mahaifin Babban Dan Siyasa da Wasu Mutum 6

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Abuja, Sun Sungume Mahaifin Babban Dan Siyasa da Wasu Mutum 6

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Yewuti na ƙaramar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja
  • Ƴan bindigan wanda suka kai harin cikin dare sun yi awon gaba da mahaifin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar
  • Wasu mutum shida na daga cikin mutanen da ƴan bindigan suka sace a yayin harin, yayin da suka harbe mutum ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mahaifin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwali, Mohammed Yakubu, a birnin tarayya Abuja.

Miyagun ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu mutum shida da ba su ji ba, ba su gani ba a yayin harin.

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja
'Yan bindigan a yayin harin sun sace mahaifin mataimakin karamar hukumar Kwali Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Aminiya ta tattaro cewa ƴan bindigan sun bindige mutum ɗaya sannan suka sace wasu mutum shida ciki har da wata mata mai ɗauke da juna biyu a ƙauyen Yewuti na ƙaramar hukumar ta Kwali.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka babban malamin addini sun yi awon gaba da matarsa a wani sabon hari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai ba shi ne karon farko da ƴan bindiga ke kai farmaki a ƙauyen ba, inda ko a watan Afirilu sun taɓa kai hari tare da sace mutum 29.

Yadda harin ya auku

Wani mazaunin garin mai suna Ibrahim Danjuma, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa ƴan bindigan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun shigo ƙauyen ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare.

Ya bayyana cewa miyagun ƴan bindigan sun shiga gidaje uku a ƙauyen ciki har da na mahaifin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, inda suka yi awon gaba da shi tare da wasu mutum shida.

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kuma harbe wani mutum mai suna Hussaini Kure wanda ya so ya tsere.

A halin da ake ciki dai ƴan bindigan sun buƙaci da biya su kuɗaɗen fansa har N30m.

Kara karanta wannan

Mutum 1 ya rasu yayin da matasa suka yi fito na fito da 'yan bindiga bayan sun yi yunkurin kai hari

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, ta bayyana cewa tana coci.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Babban Fasto

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Damakasuwa na ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka faston cocin ECWA, Amako Maraya, tare da yin awon gaba da matarsa ta aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel