Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Bala Mohammed a Matsayin Zababben Gwamnan Bauchi

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Bala Mohammed a Matsayin Zababben Gwamnan Bauchi

  • Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed a zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar a watan Maris, 2023
  • Kotun ta ce wanda ya shigar da karar, Sadique Abubakar, ya gaza gabatar da hujjoji da za su tabbatar da zarge-zargen da ya yi
  • Kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar Mohammed, sai dai Abubakar ya daukaka kara yana kalubalantar hukuncin kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Juma’a ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a zaben gwamnan jihar.

An gudanar da zaben jihar ne a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Alkali ya umurci a bai wa Emefiele masauki a gidan yarin Kuje

Dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sadique Abubakar, ya daukaka karar biyo bayan hukuncin kotun kararrakin zabe da ta tabbatar da nasarar Mohammed.

Sadique Abubakar, Bala Mohammed
Kotun daukaka karar ta yi watsa da bukatar Abubakar na soke zaben jihar Bauchi, ta kuma tabbatar da nasarar Mohammed Hoto: Sadique Abubakar / Bala Mohammed
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’ar kotun ya karanta hukuncin ne a kan korafin da mai daukaka karar ya shigar gaban kotun.

Sadique ya gaza gabatar da kwararan hujjoji

A kara ta daya, mai shigar da karar ya roki a soke zaben saboda ba a cike fom da takardun da aka yi amfani da su a zaben yadda ya kamata ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kotun ta yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujjoji kan wannan zargi.

Rahotan Vanguard ya nuna cewa, kotun ta ce wanda ya shigar da karar ya kasa bayyana akwatunan zaben da aka aikata laifukan da ya ke zargi, kuma ya kasa bayyana abin da aka cire daga fom din.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun haramta murna ana shirin yanke hukunci a shari’ar zaben gwamna

Kotu ta ba Bala Mohammed nasara

Ta kuma kara da cewa, wanda ya shigar da karar ya kasa tabbatar da yadda takardun cike fom din da ya ce na da matsala suka shafi sakamakon zaben.

A karshe dai kotun daukaka karar ta yanke hukuncin cewa Mohammed ne ya lashe zaben gwamna jihar Bauchi.

Kotun daukaka kara ta tsige Abba Kabir daga kujerar gwamnan Kano

A shari'ar jihar Kano kuwa, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa kotun daukaka kara ta tsige Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano.

Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun karar zabe ta yanke na ayyana Nasiru Gawuna a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel