Gwamnan Bauchi: Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Bala Mohammed a Matsayin Gwamnan Jihar Bauchi

Gwamnan Bauchi: Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Bala Mohammed a Matsayin Gwamnan Jihar Bauchi

  • Kotun zaben gwamnan Bauchi ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed a zaben ranar 18 ga watan Maris da aka yi a jihar
  • Kotu ta yi watsi da karar da APC da dan takararta, Air Marshal Sadique Abubakar suka shigar a gabanta
  • Kwamitin mutum uku na kotun zaben sun ce an gudanar da zaben Bala Mohammed daidai da doka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi - Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan jihar Bauchi ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris da aka yi a jihar.

Kotun zaben ta kori karar da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta na gwamna, Air Marshal Sadique Abubakar suka shigar.

Kotu ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed a matsayin gwamnan jihar Bauchi
Gwamnan Bauchi: Kotun Zabe Ta Tabbatar Da Bala Mohammed a Matsayin Gwamnan Jihar Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

An gudanar da zaben gwamnan Bauchi bisa doka, kotun zabe

Kara karanta wannan

Manyan Dalilai 3 Da Suka Sa Kotun Zaben Kano Ta Tsige Abba Gida Gida Daga Kujerar Gwamna

Bayan tataunawa sosai tare da yin nazari sosai kan shaidun da bangarorin biyu suka gabatar, kotun ta bayyana cewa babu wata kwakkwarar hujja da ke tabbatar da ikirarin da dan takarar na APC ya yi, rahoton Politics Nigeria.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotun ta riki cewa babu wani kwakkwaran dalili da zai sa a soke zaben kasancewar an gudanar da zaen daidai da tanadin doka, Channels TV ta rahoto.

Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Justis P.T Kwahar ne suka yanke hukuncin.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan bayan ya samu kuri'u 525,280 wajen lallasa abokin adawarsa kuma tsohon shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Abubakar wanda ya samu kuri'u 432,272.

Zaman yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano kai tsaye daga kotu

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Sauraran Korafe-korafen Zabe Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Da Ake Na Gwamnan jihar Arewa

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa a yau Laraba, 20 ga watan Satumba, 2023, Kotun sauraron ƙararrakin zabe zata yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano.

Jam'iyyar APC da ɗan takararta na gwamna, Nasir Yusuf Gawuna, ne suka shigar da ƙara a gaban Kotun suna kalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.

Rahoton Aminiya ya nuna cewa Gawuna, wanda ya zo na biyu a sakamakon zaben, da APC suna zargin cewa takarar Abba Gida-Gida ba ta halasta ba saboda bai zama mamban NNPP ba lokacin da aka tsayar da shi takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel