Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu 3 a Jihar Kebbi

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu 3 a Jihar Kebbi

  • Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun kai mummunan hari karamar hukumar Bunza ta jihar Kebbi
  • Maharan sun sheke mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu uku a yayin harin da ya afku a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta sha alwashin ceto wadanda aka sace

Jihar Kebbi - Wasu tsagerun yan bindiga sun halaka mutane biyu sannan suka yi garkuwa da wasu uku a kauyen Kanzanna da ke karamar hukumar Bunza ta jihar Kebbi.

Nafi’u Abubakar, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, ya tabbatar da harin, jaridar TheCable ta rahoto.

Yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Bunza ta jihar Kebbi
Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu 3 a Jihar Kebbi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Abubakar ya ce yan bindigar sun kai hari kan kauyen ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an Tsaron Haɗin Gwiwa Sun Yi Artabu da Makiyaya, Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu

Kwamishinan yan sanda ya sha alwashin ceto wadanda aka sace

Kakakin yan sandan ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Chris Aimiono-Wane, ya ziyarci kauyen sannan ya yi wa al'ummar yankin jaje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, kwamishinan yan sandan ya yi Allah wadai da harin sannan ya bai wa yan uwan wadanda abun ya ritsa da su tabbacin cewa rundunar za ta ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce tawagar hadin gwiwa na masu yaki da garkuwa da mutane da masu yaki da ta'addanci zuwa yankin.

Ya kara da cewar a yanzu haka jami'an yan sanda na kakkabe dazuzzuka, hanyoyi da wuraren da ake zargin mabuyar yan bindigar ne domin gano su da ceto wadanda aka sace, rahoton Premium Times.

Da suke martani a lokuta daban-daban, Muhammadu Jabbo, hakimin Tilli da Umar Ahmed, shugaban karamar hukumar Bunza da Yusuf Tilli, dan majalisar yankin, sun gode ma kwamishinan yan sandan kan ziyarar.

Kara karanta wannan

Kakakin Yan Sanda: "Duk Dan Sanda Da Ya Yi Wa Yan Najeriya Kwacen Kudi Dan Fashi Ne"

Sun yi kira ga mazauna yankin da su taimakawa yan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen tsamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Yan bindiga sun sace mutane da yawa a karamar hukumar jihar Kano

A wani labarin, mun ji cewa cewa har yanzun ba a tantance yawan mutanen da yan bindiga suka sace da waɗanda suka kashe ba a ƙauyen Yola, ƙaramar hukumar Ƙaraye a jihar Kano.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, hakan ya faru ne bayan jerin hare-haren da 'yan bindigar suka kai ƙauyen a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel