Yadda Dattijo Mai Shekaru 71 Ya Killace Kansa Saboda Tsoron Mata, Ya Shafe Shekaru 55 a Gida

Yadda Dattijo Mai Shekaru 71 Ya Killace Kansa Saboda Tsoron Mata, Ya Shafe Shekaru 55 a Gida

  • Callitxe Nzamwita ya yi alfahari da kulle kansa a gidansa tun yana dan shekara 16 don ya daina hulda da mata
  • Dattijon mai shekaru 71 ya ce mata na tsorata shi, sannan har ya gina katanga a gidansa don han gujewa yi masu magana ko haduwa da su
  • Ya ce ya kasance a cikin gidan tsawon shekaru 55 yayin da yake gujewa mata

Wani mutum mai shekaru 71 a duniya wanda bai taba sanin 'ya mace ba ya yi nasarar killace kansa a cikin gidansa tsawon shekaru 55 don gujewa mata.

A cewar Afrimax English, Callitxe Nzamwita ya gina katanga mai tsawon sahu 15 a kewaye da gidansa da ke Rwanda domin hana mata da jama'a isa gare shi.

Ya shafe shekaru 55 a gida don gujewa mata
Yadda Dattijo Mai Shekaru 71 Ya Killace Kansa Saboda Tsoron Mata, Ya Shafe Shekaru 55 a Boye Hoto: Afrimax English.
Asali: UGC

Ya killace kansa a gida saboda tsoron mata

Dattijon ya yarda cewa yana matukar tsoron ganin mata suna zuwa gidansa, don haka ya killace kansa.

Kara karanta wannan

“Akwai Sirrika Da Yawa”: Wata Mata Da Ta Duba Wayar Mijinta Ta Sharbi Kuka a Bidiyo, Ta Ba Mata Shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da tsoronsa, matan yankin ne ke kula da mutumin da taimaka masa. Sune suke kai masa kayan masarufi amma baya bari matan su zo kusa da shi ko kadan.

Ya ce:

"Dalilin da yasa nake rufe kaina a nan da kuma gina katanga a gidana saboda ina so na tabbatar da ganin cewa mata ba su zo kusa dani ba."

Wata mazauna yankin da ba a bayyana sunanta ba ta ce:

“Abin mamaki duk da cewa yana tsoron mata, mu ne muke taimaka masa ya samu abinci da wasu abubuwan da yake bukata, idan ka yi kokarin taimaka masa ba ya son mu matso kusa ko magana da shi.
"A maimakon haka, mukan ba shi abubuwa ta hanyar jefa su cikin gidansa, sannan ya zo ya dauke su, ba ya barin mu kusa da shi, amma duk da haka yana daukar abin da muka ba shi daga nesa."

Kara karanta wannan

“Wannan Aure Akwai Matsala”: Rudani Yayin da Bidiyon Wani Ango Da Amarya Ya Jefa Mutane Cikin Damuwa

Idan ya hango mata a hanyarsu ta zuwa gidan, Callitxe kan yi saurin rufe kansa a ciki sannan ya rufe kofar bayansa.

Mutumin wanda bai taba sanin diya mace ba yana fama ne da wata lalura ta tsoron mata da rashin son ganinsu.

Duk da taimakon da suke yi masa na yau da kullum, matan kauyen ba za su iya yin magana da Callitxe ba, wanda ke kin mata idan sun zo.

Mata ta sharbi kuka bayan duba wayar mijinta

A wani labari na daban, wani bidiyo mai ban tausayi ya nuno wata matashiyar mata cikin hawaye bayan ta duba wayar abokin zamanta a boye.

Bayan abun da ya faru da ita, matashiyar matar ta shawarci sauran mata da kada su kuskura su duba wayar abokan zamansu idan har suka samu miji nagari.

Wannan al'amari ya haifar da cece-kuce a dandalin TikTok game da mutunta sirrin juna a zamantakewa, inda wasu suka ce akwai bukatar duba wayar abokin zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng