Bidiyon ‘Dan Saurayi Da Ya Yi Karfin Hali, Ya Karbi Lambar Wayar Budurwa a Taro

Bidiyon ‘Dan Saurayi Da Ya Yi Karfin Hali, Ya Karbi Lambar Wayar Budurwa a Taro

  • Wani saurayi da wata ‘yar budurwa sun zama abin magana a shafukan sada zumunta
  • Hakan ya faru ne bayan an ga yaron ya nemi lambar wayar budurwar a bainar jama’a
  • Abin ka da yaran zamani, yarinyar ta karbi salular yaron, ana tunanin ta ba shi lamba

Nigeria - Wani bidiyo yana yawo a kafofi da dandalin sada zumunta na zamani inda aka ga wani yaro ya tambayi yarinya ta ba shi lambar wayarta.

Kamar yadda bidiyon da aka wallafa a shafin Northern Blog ya nuna, da alama wata yarinya da ta zauna kusa da karamin saurayi ta ja hankalinsa.

Shi kuwa wannan yaro bai yi wasa ba, nan take ya mika mata wayarsa domin samun lambar wayarta, hakan zai ba shi damar kulla wata alaka.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kame matashin da ya kwace waya, ya bi mata da gudu zai soka mata wuka a Kano

Za a fahimci hakan ta yadda ya mikawa yarinyar wayar da yake rike da ita, da yake ta gane inda aka dosa, bayan ‘dan jinkiri sai ta karbi wayar salular.

Lambar waya ta fito

Kafin ka ce mene, wannan Baiwar Allah tayi wasu ‘yan latse-latse a wayar matashin, ana zargin cewa a nan ta rubuta masa lambar da zai iya samunta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Cikin wani salo, yarinyar ta dawo masa da wayarsa ta bayan hannu ba tare da jama’a sun lura ba.

Babu tabbas game da inda abin ya faru dai ko ranar da ya faru, watakila a wajen bukukuwan nan ne da aka shirya a lokutan sallah a makon jiya.

Sauti ya cika wurin saboda haka ba a iya jin gajerar tattaunawar da ta wakana tsakaninsu ba.

Yarinya da yaro 'yan kwalisa

Kara karanta wannan

Namijin duniya: Lakcara mai mata hudu ya girgiza intanet, hotunansa da, matasa da 'ya'yan sun ba da sha'awa

Shi dai wannan yaro ya cakara hula dauke da farar shadda yayin da yarinyar ta ci gayu da atamfa da karamin gyale kamar dai yadda aka saba a Arewa.

Yayin da shi yake tare da wasu abokansa a wajen, babu tabbacin ‘yar budurwar ta na zaune ita kadai ne ko na tare da wani saurayin ko kuwa kawayenta.

Kamar yadda wasu masu tofa albarkacin bakinsu su ka fada, yarinyar ta na zaune da wani dabam.

Su kan su abokan wannan Bawan Allah sun tabbatar da kasadarsa a fili, yana samun lambar wayar, shi kuwa ya tada keyarsa, ya kama hanyar gabansa.

Martanin mutane a Twitter

Kabeer Jameel ya rubuta:

“Ka ji tsoron Allah...kaji tsoron mata”

Ali Abba:

"Ta na tare da wani fa"
Jira kawai yake ya amsa ya warey

- @Bichi_Nazeer

Gayu ikon Allah

- @HabuSadeik

Ga bidiyon nan a kasa:

Kara karanta wannan

Maganinki: Lakcara ya ba daliba 0 a jarrabawa saboda ta yi amfani da ChatGPT

Asali: Legit.ng

Online view pixel