“Da Ciwo Sosai”: Wata Mata Da Ta Duba Wayar Mijinta a Boye a Sharbi Kuka a Bidiyo

“Da Ciwo Sosai”: Wata Mata Da Ta Duba Wayar Mijinta a Boye a Sharbi Kuka a Bidiyo

  • Wani bidiyo da ya yadu ya nuno wata matashiyar mata cikin kuka bayan ta duba wayar mijinta
  • Bidiyon ya haddasa cece-kuce a kan baun yi wa mutum kutse a al'amuransa da muhimmancin yarda a zamantakewa
  • Kawunan mutane ya rabu kan ko duba wayar abokin zama yana nufin rashin yarda ko kuma hanya ce ta duba zamantakewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A cikin wani bidiyo mai ban tausayi, an gano wata matashiyar mata cikin hawaye bayan ta duba wayar abokin zamanta a boye.

Bayan abun da ya faru da ita, matashiyar matar ta shawarci sauran mata da kada su kuskura su duba wayar abokan zamansu idan har suka samu miji nagari.

Matar aure ta sharbi kuka bayan ta duba wayar mijinta
“Da Ciwo Sosai”: Wata Mata Da Ta Duba Wayar Mijinta a Boye a Tsharbi Kuka a Bidiyo Hoto: @yabaleftonline/instability.
Asali: Instagram

Matar da ta duba wayar mijinta ta haddasa cece kuce a soshiyal midiya

Wannan al'amari ya haifar da cece-kuce a dandalin TikTok game da mutunta sirrin juna a zamantakewa.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Matar aure ta haifi tagwaye kasa da awanni 24 bayan mutuwar mijinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu sun yi korafin cewa duba wayar miji rashin yarda ce, yayin da wasu ke ganin yana iya ba mutum damar sanin zunuban da abokin zamansa ke aikatawa da kuma ainahin dabi'unsa.

Jama'a sun yi martani a kan duba wayar miji

Da suka martani kan bidiyon, jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin.

Da dama sun yi gargadi a kan bankado sirrin mutum sannan suka jaddada muhimmancin yarda da zama a tattauna.

Sun nanata cewa ya kamata a gina yarda a kan tattaunawa ta gaskiya da kuma mutunta juna, maimakon yi wa mutum kutse a wayarsa.

@ble_ssing_sunday ta yi martani:

"Duba wayar abokin zamanka dole ne wasu lokutan don sanin inda ya ajiye ka a rayuwarsa! Ya fi ka yi kuka yanzu fiye da ka yi kuka daga baya."

richard_hillssta ce:

"Idan ba mutumin kirki bane za ki yi kuka idan kika duba wayarsa."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya siya wayar iPhone 15 amma ya tarar da teba a kwalin, ya koka a bidiyo

@lukasporo ta ce:

"Duba wayar abokin zamanki a matsayinki na mace yana da kyau wasu lokutan don ki san yadda yake darajaki kada ki je ki biyewa dadin baki."

"Akwai matsala": Bidiyon wani ango da amarya ya jefa mutane cikin tunani

A wani labarin, mun ji cewa bidiyon wasu sabbin ma’aurata ya ta da kura a soshiyal midiya. An gano ango da amaryar suna kiciniyar fita daga kofa a lokacin guda ba tare da sun dagawa juna kafa ba.

Jama’a da dama sun hango tarin kalubale a wannan gidan auren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel