Sama Da ’Yan Ta’adda 100 Ne Suka Mutu a Yakin da Ya Barke Tsakanin Boko Haram da ISWAP Borno

Sama Da ’Yan Ta’adda 100 Ne Suka Mutu a Yakin da Ya Barke Tsakanin Boko Haram da ISWAP Borno

  • Rahoton da muke samu daga jihar Borno ya bayyana yadda ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ke kashe kansu a Marte
  • Wannan na zuwa ne a wani yakin daukar fansa da ke faruwa tsakanin tsagerun biyu da suka addabi al’umma
  • Boko Haram ta shafe shekaru tana aikin barna a yankin Arewa masu Gabas da ma wasu jihohin yankunan Arewa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Marte, jihar Borno - A rikicin da ya barke tsakanin bangaren Bakoura Buduma na Boko Haram da na ISWAP an ce an kashe 'yan ta'adda sama da 100 a tafkin Chadi da ke yankin Marte a jihar Borno.

An tattaro cewa fadan wanda ya fara da misalin karfe 12 na daren ranar Asabar, yana ci gaba da gudana har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto a wani wuri mai suna Bakuram da ke gabar tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Hukunta Wike da Sauran Jagororinta da Su ka Yi wa Tinubu Aiki

Kafar labaran tsaro ta Zagazola Makama ta fahimci cewa, kungiyar ISWAP na daukar fansa ne a kan sace mayakanta 60 da kwamandoji uku da kungiyar Boko Haram ta yi.

Yan ta'addan Boko Haram da ISWAP na can suna kashe kansu
Yadda 'yan ISWAP da Boko Haram ke kashe kansu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rikicin na baya-bayan nan, a cewar majiyoyi, ya samu jagorancin wani Abou Idris, tsohon shugaban tsara yaki na Boko Haram ta Bakoura wanda ya bar su ya koma ISWAP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Irin asarar rayukan da aka yi

Majiyar ta bayyana cewa, an samu asarar rayuka daga bangarorin biyu amma kungiyar ta ISWAP ta fi kashe ‘yan ta’addan na Boko Haram da yawa.

A cewar majiyar:

"Yayin da muke magana a yanzu haka ana ci gaba da gwabzawa kuma an kashe 'yan ta'adda sama da 100 daga bangarorin biyu.”

Ana ci gaba da samun zama mai tsami tsakanin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

ISWAP Ta Kalubalanci Yan Boko Haram Don Fafatawa A Dajin Sambisa

Manyan ‘yan ta’adda sun mika wuya

A wani labarin, ‘yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun mika wuya ga rundunar dakarun hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a jihar Borno.

‘Yan ta'addan wadanda suka hada da kwamandoji 4 da mayaka 13 tare da iyalansu 45 ne suka mika wuya ga dakarun sojojin.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar MNJTF, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan ta'addan sun mika wuya ne bayan rundunar ta kara kaimi wajen ragargazarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel