"Ba Zamu Nemi Sulhu da Yan Bindiga Ba" Gwamnatin Katsina Ta Magantu

"Ba Zamu Nemi Sulhu da Yan Bindiga Ba" Gwamnatin Katsina Ta Magantu

  • Gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa ba za ta tattauna da 'yan bindiga don neman sulhu ba
  • Kwamishinan tsaro da harkokon cikin gida, Mu'azu Ɗanmusa ya jaddada kudirin gwamnatin Dikko na kawo karshen 'yan bindiga a jihar
  • A cewarsa, kaddamar da sabuwar rundunar 'yan sa'kai alama ce ta zahiri da ke nuna yadda Radɗa ya maida hankali kan tsaro

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta ce ba za ta tattauna da duk wani ɗan ta'adda ko kungiyar 'yan bindiga ba, amma za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare al’umma.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Muazu-Danmusa, ne ya bayyana haka a wata hira da hukumar dillancin labarai NAN ranar Laraba.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda.
"Ba Zamu Nemi Sulhu da Yan Bindiga Ba" Gwamnatin Katsina Ta Magantu Hoto: Dr. Dikko Radda
Asali: Facebook

Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin Malam Dikko Raɗda na ganin an kawo karshen ‘yan fashin daji da sauran matsalolin tsaro, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Gano Asusun Banki Fiye Da 570 Da Tsohon Gwamnan PDP Ya Ɓoye Kafin Ya Sauka Mulki a Arewa

Muazu-Danmusa ya kuma ce gwamnatin na daukar matakan da suka dace domin bai wa ‘yan gudun hijirar jihar damar komawa garuruwansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kaddamar da rundunar Community Security Watch Corps (KCSWC) da Gwamna Raɗɗa ya yi ranar 10 ga watan Oktoba, alama ce da ke nuna yadda ya ɗauki sha'anin tsaro.

An fara shirin maida 'yan gudun hijira gidajensu

A rahoton Premium Times, Kwamishinan ya ce:

"Ina tunanin jihar Katsina ce tafi kowacce jiha yawan ‘yan gudun hijira a yankin Arewa maso Yamma sakamakon rashin tsaro. Duk da haka, muna ƙoƙari canza labarin ta hanyar tsara dabarun za su magance matsalar."

Muazu-Danmusa ya ƙara da cewa gwamnati ta tsara daidaita albashin dakarun KCSWC bisa tsarin mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.

"Muna kan gina musu ofisoshi, mun ba su motocin sintiri, babura, makamai da sauran kayan aiki domin inganta ayyukansu."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Gidan Ɗan Majalisar Arewa, Sun Tafi da Matarsa da 'Ya'yansa

"Muna tafiya daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar nan wajen samar musu da dukkan wadannan abubuwa," In ji shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa dakarun rundunar sun shirya tsaf wajen yin wannan aiki na sadaukar da rayuwarsu domin kare dangi da al'ummarsu.

Zan Iya Sadaukar da Rayuwata Domin Kawo Karshen Yan Bindiga a Katsina, Radda

Kuna da labarin Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare rayukan al'ummar jihar Katsina

Gwamnan ya ce tsaro shi ne abin da gwamnatinsa ta fi ba fifiko bisa haka ya yi dokar kafa rundunar tsaron da ya kaddamar kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel