Zan Iya Sadaukar da Rayuwata Domin Kawo Karshen Yan Bindiga a Katsina, Radda

Zan Iya Sadaukar da Rayuwata Domin Kawo Karshen Yan Bindiga a Katsina, Radda

  • Malam Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin Ƙatsina ta samu zaman lafiya
  • Gwamnan ya ce tsaro shi ne abin da gwamnatinsa ta fi ba fifiko bisa haka ya yi dokar kafa rundunar tsaron da ya kaddamar
  • Ya ce 'yan sa'kan da aka dauka sun amince zasu yi aiki don kare mutuncin, iyaye, iyalai da danginsu daga ta'addancin 'yan bindiga

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin kawo karshen ayyukan ta'addancin yan bindiga a jihar.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Gwamna Raɗɗa ya ce tsaro shi ne abu mafi muhimmanci kuma bisa haka ne ya kafa dokar kirkiro da rundunar tsaron jiha, waɗanda aka ba su makamai.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Gidan Ɗan Majalisar Arewa, Sun Tafi da Matarsa da 'Ya'yansa

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda.
Zan Iya Sadaukar da Rayuwata Domin Kawo Karshen Yan Bindiga a Katsina, Radda Hoto: Dikko Radda Ph. D
Asali: Facebook

Gwamnan, wanda a makon da ya gabata ya kaddamar da jami'an tsaro 'yan sa'kai, ya ce za su taimaka wa hukumomin tsaro a kokarin tabbatar da zaman lafiya.

A ruwayar Daily Trust, Dikko Raɗda ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun kaddamar da su, mun ba su horarar wa da makamai, sun ba su kayan aiki da motoci, Babura har da motoci masu sulƙe domin inganta aikin da zasu yi."

Yadda zamu bai wa 'yan sa'kai alawus - Radɗa

Dangane da alawus-alawus ɗin da za a riƙa ba su, gwamnan ya ce gwamnati ta amince da tsarin mafi karancin albashi, kuma za a biya 'yan sa'kan daidai da tsarin.

"Jama'a su sani cewa wadannan dakarun suna yin wannan aikin ne ba tare da biyansu albashi ba kuma suna da kwarin gwuiwa don kare iyalansu da al'ummarsu."
"Maganganun da wasu suke yi cewa irin waɗan nan 'yan sa kan ne ke ƙara kawo taɓarɓarewar tsaro ba gaskiya bane, mazauna garuruwan da abin ya shafa sun san komai."

Kara karanta wannan

"Ku Kirkiri Doka Da Za Ta Tilastawa Ma'aikatan Gwamnati Kara Aure", Babban Malami Ya Shawarci Majalisar Jigawa

"Kuma ba zai yiwu mu bari waɗan nan bara gurbin 'yan bindigan su ci gaba da cin karensu ba bu babbaka ba, suna kashe mutane kuma suna garkuwa da wasu."
“Na rantse da Allah, a matsayina na gwamna, ko da zan rasa rayuwata, ba zan bari wani ya zo ya cutar da jama’ata ba. Matsalar ‘yan bindiga ta kai matsayin da ya kamata mu hada kai mu kawo karshenta."

- Malam Dikko Raɗda.

Wannan kalamai na Radda sun haddasa cece kuce tsakanin mutanen Katsina, wasu na ganin ga dukkan alamu zai cika alƙawarin da ya ɗauka wasu kuma cewa su ke an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa.

Malam Yahuza, ɗan jihar Katsina kuma Malamin Musulunci ya faɗa wa Legit Hausa cewa ba abinda zasu ce sai fatan Alheri ga mai girma gwamna.

"Ba zan manta ba, a lokacin kamfe ya ce da shi za a riƙa shiga daji, yanzu kuma ya sake maimaita wa, muna fatan dai Allah ya cika masa burinsa mu samu zaman lafiya a Katsina."

Kara karanta wannan

Auren Gata: "Ku Guji Duba Wayoyin Abokan Zamanku", Kwankwaso Ga Angwayen Kano

Kabir Abdullahi, mamban PDP cewa ya yi an jima ana ruwa ƙasa da shanye wa, ba yau Dikko ya fara wannan maganar ta shiga daji ba kuma zancen zai bada rayuwarsa magana ce kawai.

Jami'an Tsaro Sun Mamaye Sakateriyar Jam'iyyar PDP a Jihar Ondo

A wani rahoton kuma Jami'an tsaro sun kwace iko da babbar Sakateriyar jam'iyyar PDP da ke Akure babban birnin jihar Ondo da safiyar ranar Litinin.

Rahoto ya nuna cewa yan sanda da DSS sun kewaye babbar ƙofar shiga yayin da matasan PDP ke shirin fara zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel