Yin Jima'in Kure Juna Na Kawo Targaden Azzakari, Likitocin Al'aura

Yin Jima'in Kure Juna Na Kawo Targaden Azzakari, Likitocin Al'aura

  • Matasa majiya karfi kan shiga cacan yin jima'in kure da yan mata majiya karfi irinsu
  • Lokuta da dama, an samu labarin mazajen da ke rasa rayukansu yayinda suke cikin yanayin sharholiya
  • Likita ya bayyana cewa duk namijin da ya samu targade a azzakari da yiwuwan shikenan ba zata sake aiki ba
  • Kwanakin baya a unguwar Kubwa birnin tarayya Abuja wani mutumi ya mutu a dakin Otal da wata

Likitoci a fannin lafiyar azzakari sun gargadi Maza kan yin jima'in kure juna da Mata saboda hakan na iya hallaka mazakutansu gaba daya.

Masanan sun bayyana cewa maza masu jima'in kure na iya arangama da targaden azzakari kuma jinyarsa na da wuyan gaske.

Sun kara da cewa hakazalika masu amfani da kwayoyin karin karfi na iya hallaka kawunansu.

Punch HealthWise ta zanna da Likitoci kuma sun yi jawabi kan lamarin.

Kara karanta wannan

Matsanancin Halin Talaucin da za ka bar mu Ciki ya fi Wanda ka Tarar da mu, Kukah ga Buhari

Dr. Gabriel Ogah, babban masanin ilmin mazakuta kuma Dirakta Manajan asibitin Ogah Hospital and Urology Centre, Fugar, jihar Edo ya bayyana cewa yin jima'in kure na iya hallaka namiji har barzahu.

Yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ko shakka babu, jima'in kure na iya kashe mutum. Yana iya lalata zuciyar mutum idan ba isasshen lafiya garesa ba."
"Jima'in kure na kawo kamewar azzakari wanda turawa ke kira ga priapism musamman masu hadawa da kwayan karin karfi."
"Priapism shine yanayin da azzakari zai tashi kuma yaki saukowa. Idan mutum ya sha kwaya, azzakari na iya kamewa yaki sauka."
"A shekarar nan kadai, na yi jinyar mutum hudu da azzakarinsu ya daskare ya ki saukowa. Sai an yiwa azzakarin aiki yake iya kwanciya."
"A shekaru biyu da suka gabata, na kula da mutane da suka samu targade yayin jima'i."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Kwana 1 da kashe tarin mutane, 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a Arewa

Banana
Yin Jima'in Kure Juna Na Kawo Targaden Azzakari, Likitocin Al'aura

Azzakari na iya targade

Likitan ya yi kira ga Mazaje su yi hattara saboda Azzakari na iya targade idan ya mike.

Yace:

"Na yiwa wani aikin tiyata watanni hudu da suka gabata, azzakarinsa ya balle biyu, mafitsarar ta kaste biyu."
"Idan kuma ba'a yiwa mutum aikin tiyata cikin sa'o'i 24 ba, shikenan azzakari ba zai sake aiki ba har abada."
Mun fi fuskantar wannan matsalar da Matasa. Yan shekara 18 zuwa 30 ne wannan abu ya fi shafa

Ya bada shawaran cewa:

"Ku daina amfani da kwayoyin kara karfi musamman idan ba Likita ya baka ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel