Kotu Ta Daure Malami a Kurkuku Saboda Ya Zane Daliba Mace da Bulala

Kotu Ta Daure Malami a Kurkuku Saboda Ya Zane Daliba Mace da Bulala

  • Kotu ta bada umarnin a tasa wani Malamin makarantar Sakandiren mata zuwa gidan Yari bisa zargin lakaɗa wa ɗalibarsa bugun tsiya
  • Alkalin Kotun mai zama a Wuse II Abuja ya amince da bada belin wanda ake zargin kan N2m da kuma masu tsaya masa
  • Tun da farko, hukumar yan sanda ta gurfanar da Malamin makarantar a gaban Kotu, ta zayyano laifuka 2 da ake zarginsa

FCT Abuja - Hukumar 'yan sandan Najeriya ta gurfanar da wani malamin makaranta ɗan kimanin shekara 43, David Yusuf, a gaban Kotun Majistire mai zama Wuse II a Abuja ranar Taata.

Jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta na Manhajar X cewa an gurfanar da Malamin ne bisa tuhumar ya zane ɗaliba mace a makarantar Sakandiren mata da ke Kuje.

Kotu ta ɗaure Malamin makaranta.
Kotu Ta Daure Malami a Kurkuku Saboda Ya Zane Daliba Mace da Bulala Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Malamin wanda aka ce ma’aikaci ne na wucin gadi a makarantar, ana tuhumarsa da laifuka biyu, jikkata ɗalibar ba tare da dalili ba da kuma cin zarafi.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Laifi biyu da ake tuhumar Malamin da aikata wa

Ɗan sanda mai shigar da kara, Edwin Inegbenoise, ya faɗa wa kotun cewa kes din ya baro Caji Ofis din Kuje, zuwa sashin binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa wani mazaunin rukunin gidajen Union Homes a Kuje mai suna, Henry Lotim, ne ya kai ƙara caji Ofis ɗin 'yan sanda kan abin da aka yi wa diyarsa.

Inegbenoise ya ce mutumin ya faɗa wa 'yan sanda cewa Malamin ya ci zarafin ɗiyarsa 'yar kimanin shekara 16 a duniya, wacce ke karatu a makarantar ranar 2 ga watan Yuni.

Ya kara da cewa a lokacin karatun dare, malamin ya laƙaɗa wa ɗalibar dukan tsiya da sandar ƙarfe, tare da raunata ta a tafin hannu da sauran sassan jikinta.

Daga ƙarshe ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya faɗa wa Kotu cewa laifukan da ake zargin malamin da aikatawa sun saɓa wa sashi na 241 da 326 na kundin Fenal kod.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Sabon Nadin Mukami Mai Muhimmanci a Hukumar FCTA

Kotu ta bada belinsa bisa sharuɗɗai

Alkalin kotun, Abdulmajid Oniyangi, ya amince da bada belin wanda ake ƙara kan kudi naira miliyan biyu tare da mutane biyu da za su tsaya masa mazauna yankin Kotun.

Ya ce dole rijistaran Kotun ya tantance waɗanda za su tsaya wa Malamin gabanin a sake shi daga gidan Kurkuku. Daga nan ya ɗage zaman zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba.

Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Batun Tsige Mataimakin Gwamnan APC

A wani rahoton na daban Mataimakin gwamnan jihar Ondo da ke fuskantar barazanar tsige shi ya yi rashin nasara a babbar Kotun Akure.

A hukuncin da ta yanke kan ƙarar da ya shigar, Kotun ta ce ba ta hurumin kawo abin ka iya haddasa cin karo a ɓangaren shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel