Bidiyo: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Yayin da Mai Aiki Ta Kona Mata Fuska, Ta Zuba Sinadari a Man Shafarta

Bidiyo: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Yayin da Mai Aiki Ta Kona Mata Fuska, Ta Zuba Sinadari a Man Shafarta

  • Wata matashiyar yar Najeriya a TikTok ta bayyana abun da mai aikin da mahaifiyarta ta kawo daga kauye ta yi mata
  • A wani bidiyo da ya yadu, budurwar ta nuna yadda fuskarta yake luwai-luwai kafin yar aikin ta kona ta
  • A cewarta, mai aikinsu ta fallasa cewa ita ta zuba mata wani abu a man fuskarta wanda ya kona ta

Wata mai aiki ta sha caccaka a soshiyal midiya bayan ta zuba sinadari mai cutarwa a man fuskar wata budurwa.

Wacce abun ya ritsa da ita ta bayyana cewa mahaifiyarsu ce ta kawo sabuwar mai aikin tasu daga kauye don taimakawa da ayyukan gida.

Budurwa
Bidiyo: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Yayin da Mai Aiki Ta Kona Mata Fuska, Ta Zuba Sinadari a Man Shafarta Hoto: TikTok/@princesstorial26
Asali: UGC

Abun bakin ciki, bayan dan zama da ta yi da su, uarinyar ta kara wani sinadadi a man shafawarta wanda ya sa fuskarta ya fara konewa.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya: Mata tazo neman magani wajen boka, ya dirka mata ciki a Kano

Matashiyar ta wallafa wani bidiyonta na kafin faruwar lamarin da bayan afkuwarsa, kuma banbancin ya ba da mamaki saboda fuskarta luwai-luwai kafin faruwar abun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma yi gargadin cewa ya kamata mutane su yi taka-tsantsan saboda ba kowa ne ke nufin mutum da alkhairi ba.

Ta rubuta:

"Mahaifiyata ta samo sabuwar mai aiki daga kauye kuma ga abun da ta aikata mani, ta fallasa cewa ta kara wani abu a man fuskata."

Jama'a sun yi martani

@chibuzo_01 ya rubuta:

"Duniyar nan cike take da mugayen mutane."

@RachelleAgatha ta yi martani:

"Wasu mutanen kawai basu da godiya ne. Yi hakuri yar uwa."

@User0111654321 ya ce:

"Wannan mugunta ce karara, dan Allah ki yi wa kanki alfarma na korarta."

@Ugonnaosinachi:

"Hmmmmmm. Wannan ne dalilin da yasa bana goyon bayan zuwa daukar mai aiki daga kauye."

Kalli bidiyon a kasa:

Kara karanta wannan

Shekarunta 23: Wani Mutum Ya Wallafa Hotunansa Da Wata Mata Mai Nakasa, An ce Sun yi Aure

Uba da 'ya sun kulla yarjejeniya kan fara soyayya

A wani labari na daban, wani uba ya shiga yarjejeniya da karamar diyarsa game da lokacin da yake so ta fara kula samari da sunan soyayya.

Kamar yadda mahaifin nata ya bukata, ya ce yana so ta ci gaba da killace kanta har sai ta kai shekaru 20 da 'doriya wato sai nan da 2041.

Wannan al'amari ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya inda wasu suka ce da kyar idan ba za a karya wannan yarjejeniya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel