"Tun Jiya Na Ke Yin Aikace-Aikacen Gida": Budurwa Ta Aikatu A Gidansu Saurayinta, Ta Yi Wanke-Wanke

"Tun Jiya Na Ke Yin Aikace-Aikacen Gida": Budurwa Ta Aikatu A Gidansu Saurayinta, Ta Yi Wanke-Wanke

  • Budurwa ta zo da abin mamaki yayin da ta zama 'yar aiki a gidan surakanenta don neman wuri
  • Budurwar ta ce ta yi haka ne don neman gindin zama a gidansu saurayin nata tun ma kafin ya aure ta
  • Ta ce duba da irin wahalhalun da ta sha a gidan saurayin nata, ya zama dole su san hanyar da za su bi a aure ta

Wata budurwa ta girgiza intanet bayan ganinta a gidan su saurayinta tana aikin bauta da sauran aikace-aikace.

Budurwar ta ce tana aiki a gidan kaman matar aure tun lokacin da zata zo kuma yanzu haka ta gama galabaita, Legit.ng.

Budurwa ta zama 'yar aiki a gidansu saurayinta don samun wurin zama a wani bidiyo
Budurwar Lokacin Da Take Aikin Wahala A Gidan. Hoto: @lizzy.193.
Asali: TikTok

A wani faifan bidiyon da ta wallafa, an gano ta tana karbar umarni daga wata mata yayin da take daukar abubuwa masu nauyi.

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

Budurwar ta yi wanke-wanke da sauran aikin bauta

Bayan haka budurwar ta yi wanke-wanke da sauran aikace-aikace masu wahala inda ta ce dole a aureta a gidan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An gano ta har durkusawa karamin yaro take yi a gidan duk don samun gindin zama da neman hadin kansu.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun mai da martani akan wannan kokari na budurwar.

beautymicheal2:

"Ni da wannan aiki, su kira ni da iyawo ya isa, zan yi abin da zan iya naje na huta."

SHININGSTAR Empire:

"Mun gode da kuka nuna mana haka a intanet, bamu taba tunanin gwada haka ba."

Tí oluwa nile:

"Wannan shi ne ma'anar mata ta gari da Najeriya ta sani."

PrincessMercy:

"Dole Pablo ya yi aure, idan ba haka ba araduwa ta nemo inda yake."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Shiga Yanayi Bayan Saurayinta Ya Gudu Saboda An Yanke Mata Kafa

Omolara:

"Matar kirki kenan, banga an yi nema ba, wanda ban tsinana masa komai ba shi zai aure Ni."

Adebayo:

"A karshe karin kumallo ne, a cinye duk abubuwan ka."

AbimbolaOlokuntoye:

"Wannan zamani suna kokari, duk da wahalar da ake ciki muna neman hanyar faranta kanmu rai, bidiyon ya yi kyau."

Budurwa Ta Koka Yayin Da Saurayinta Ya Tsere Bayan Dandana Abincinta, Ba Ta San Dalili Ba

A wani labarin, wata budurwa ta rasa dalilin da yasa saurayinta ya tsere mintuna kadan bayan dandana abincinta.

Budurwar ta ce sun hadu da masoyin nata ne a kafar sadarwa inda suka shafe shekaru suna soyewa.

Abin mamaki bayan ya tsere, ya yi bulokin din budurwar ta ko ina yadda ba za ta sake neman sa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel