“Karamar Barauniya”: Matashi Ya Fusata Bayan Budurwa Ta Karbi Kudin Mota a Hannunsa Amma Ta Ki Zuwa

“Karamar Barauniya”: Matashi Ya Fusata Bayan Budurwa Ta Karbi Kudin Mota a Hannunsa Amma Ta Ki Zuwa

  • Wata matashiya yar Najeriya ta yi fice a soshiyal midiya bayan ta saki sakon WhatsApp da wani mutum ya aike mata
  • A cikin sakonsa, mutumin ya kira ta da "karamar barauniya" kan ta ki kai masa ziyara bayan ya tura mata da kudin mota
  • Lamarin ya kayatar da mutane inda suka garzaya sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu

Wata yar TikTok mai suna @_halfgirlfriend ta saki hoton hirarsu da wani mutumi wanda ya aika mata da kudin mota.

Sai dai kuma, da gangan ta ki zuwa kuma hakan ya fusata matashin wanda ya yi martani nan take.

Budurwa ta ki zuwa gidan saurayi bayan ta karbi kudin mota
“Karamar Barauniya”: Matashi Ya Fusata Bayan Budurwa Ta Karbi Kudin Mota a Hannunsa Amma Ta Ki Zuwa Hoto: @halfgirlfriend/TikTok
Asali: TikTok

Matashi ya ji radadi bayan matashiyar da ya aikawa kudin mota ta ki zuwa

Mutumin ya aika mata da sako ta WhatsApp yana mai bayyana rashin jin dadinsa kan abun da ta yi.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Hadu Da Saurayin Da Ya Yi Tattaki Daga Amurka Don Ganinta a Karon Farko a Bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Kin ba ni kunya, ke yar karamar barauniya."

Martanin jama'a kan budurwar da ta karbi kudin mota amma ta ki zuwa wajen saurayi

@top LIVE ta ce:

"Yan uwa mata na alfahari da ke."

@Nancy Andrew ta ce:

"Abun ya yi masa ciwo."

@lovelylo400 ta yi martani:

"Koya mani dabarar."

@mima ta yi martani:

"A kowani dan lokaci."

@Ashleyyyy ta yi martani:

"Yarinya ina bukatar sanin ko kin mayar da shi."

@Best ta yi martani:

"Kada akpi ya ga wannan bidiyon."

@Ibunkun ya ce:

“Baba na so ya yi kuka."

Kalli wallafar a kasa:

Ya cika mako: Budurwa ta ba da labarin yadda ta kare bayan ziyartar saurayinta

A wani labarin, wata budurwa a Najeriya ta koka kan yadda tayi tafiya mai dogon zango daga Jos har jihar Lagos don kai ziyara wurin saurayinta.

Kara karanta wannan

“Na Saduda”: Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Ci Kudinta a Gidan Caca, Bidiyon Ya Taba Zukata

Ta bayyana saurayin nata a matsayin mutum mai mako bayan ta share kwanaki a gidansa amma ko kudin mota ma bai bata ba.

Ta ce lokacin da take gidan nasa, ta kwanta jinya kuma ita tayi wa kanta magani da kudinta tun da saurayin bashi da niyyar taimakonta.

Ta ce matsalarta da saurayin shine, duk lokacin da tace tana son cin kifi ko shawarma sai yace ta kawo kudin don babu kudi a wurinsa, ta ba shi ya siyo musu amma zai fi ta ci da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel