Wata Matashiya Ta Nunawa Duniya Cikin Da Take Dauke Da Shi, Bidiyon Ya Yadu

Wata Matashiya Ta Nunawa Duniya Cikin Da Take Dauke Da Shi, Bidiyon Ya Yadu

  • An gano wata matashiyar mata dauke da tsohon ciki a wani wuri mai kama da asibiti yayin da take shirin haihuwa
  • Matar na ta kai wa da komowa wanda alamu suka nuna tana cikin nakuda ne lokacin da aka dauki bidiyon
  • Dan gajeren bidiyon ya yadu kuma mutane da dama sun garzaya sashin sharhi don yi mata fatan sauka lafiya

Akalla mutane miliyan 1.6 ne suka kalli bidiyon wata matashiyar mata wacce ke dauke da juna biyu.

Shafin @paulinmonzongodol ne ya wallafa bidiyon a TikTok kuma alamu sun nuna matashiyar na a asibiti ne.

Mutane sun yi mata fatan sauka lafiya
Wata Matashiya Ta Nunawa Duniya Cikin Da Take Dauke Da Shi, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@paulinmonzongodol.
Asali: TikTok

Matashiyar na ta kaiwa da komowa a harabar asibitin sannan tana ta tattaunawa da wasu mutane da ke wajen a takaice.

Alamu sun nuna tana motsa jikinta ne yayin da take shirin haifo dan da ke cikinta. Sai dai kuma Legit Hausa ba za ta iya tabbatar da hakan ba kasancewar bidiyon baya dauke da kowani rubutu.

Kara karanta wannan

“Yanzu Ba Sirri”: Bidiyon Wani Mutum Da Wata Yar Wada a Otel Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon wata mata da tsohon ciki ya yadu

Ana iya ganin katon cikin da take dauke da shi duk da yanayin kankantar halittarta.

A halin da ake ciki, jama'a sun yi martani sosai a kan bidiyon yayin da suka nuna sha'awar karfin gwiwar da matar ke da shi.

Yayin da wasu suka yi mata fatan alkahiri, wasu sun ce basu taba ganin wada da ciki ba a rayuwarsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da TikTok sun yi martani kan bidiyon mace mai juna biyu

@user5640192586519 ya ce:

"Kowace mace ta cancanci haihuwar da. Ka ce amin bayan ni, lokacin ki zai zo da iznin Allah."

@kendra ta ce:

"Sannan ga ni nan, mai cikakkiyar lafiya amma tsawon shekaru biyar da aure ba tare da haihuwa ba. Allah ya isar da rahamarsa a gareni."

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

@abass50 ya ce:

"Ta cancanci haka. Gidoya ga Allah da yasa ta zama uwa. Allah ya kareki yayin haihuwa."

@Chadi@032 ta ce:

"Allah ya sauke ki lafiya."

Bidiyon wani mutum da yar wada a otel ya yadu, jama’a sun yi cece-kuce

A wani labarin, mun ji cewa masu amfani da dandalin soshiyal midiya sun yi cece-kuce bayan cin karo da bidiyon wani mutum a cikin otel tare da wata yar wada.

Enigma ne ya fara yada dan gajeren bidiyon amma dai bai bayyana a ina ne aka dauki bidiyon ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel