Jarumar Fina-finan Hausa, Hajia Binta Ola Ta Rasu A Jihar Katsina

Jarumar Fina-finan Hausa, Hajia Binta Ola Ta Rasu A Jihar Katsina

  • Masana'antar Kannywood ta shiga jimami bayan rasuwar daya daga cikin jarumanta a jiya Talata
  • Marigayiya Hajiya Binta Ola ta rasu a daren jiya Talata 3 ga watan Oktoba a gidanta da ke jihar Katsina
  • Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka da safiyar yau Laraba 4 ga watan Oktoba a shafinsa na Facebook

Jihar Katsina - Jarumar fina-finan Kannywood mai suna Hajiya Binta Ola ta riga mu gidan gaskiya a Sabuwar Unguwa Kofar Kaura da ke Katsina.

Shugaban Hukumar ta ce fina-finai, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka da safiyar yau Laraba 4 ga watan Oktoba a shafinsa na Facebook.

Hajiya Binta Ola ta riga mu gidan gaskiya
Allah ya yiwa Hajia Binta Ola rasuwa a Katsina. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Yaushe jarumar Kannywood, Binta Ola ta rasu?

Ya ce za a yi sallar jana'izarta yau Laraba da misalin karfe 10 na safe a gidanta dake Sabuwar Unguwa Kofar Kaura a Katsina.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC Ta Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi Da Za Su Tattauna Da Gwamnati, Ta Yi Wa Ma'aikata Albishir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayiya Binta Ola ta rasu ne a daren jiya Talata 3 ga watan Oktoba a jihar Katsina, TRT Afirka Hausa ta tattaro.

Rahotanni sun tabbatar cewa Binta Ola ta gama shirya yin bikin Maulidi kenan a yau Laraba kamar yadda ta saba ashe ba za ta ga wannan rana ba.

An tabbatar da cewa marigayiyar ta saba gudanar da Maulidi a ko wace shekara kamar yadda ta shirya yi a yau Laraba 4 ga watan Oktoba.

Meye mutane ke cewa kan jaruma Binta Ola?

Jarumar ta yi fice musamman a shirin 'Dadin Kowa' mai dogon zango na tashar Arewa24 da kuma wasu fina-finan Hausa.

Ta yi fina-finai da dama yayin da ta ke kan kaifinta a masana'antar ta Kannywood masu fadakar da jama'a.

Masu jimami da dama sun bayyana marigayiyar a matsayin mai hakuri da kuma iya zama da mutane.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Cafke Naira Marley Kan Mutuwar Mohbad, Bayanai Sun Fito

Mahaifiyar Young Sheikh ta riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, ana cikin jimami yayin da mahaifiyar Dakta Zakeer wanda aka fi sani da Young Sheikh ta rasu.

Mijin marigayiyar shi bayyana haka a shafinsa na Facebook inda ya yi addu'ar ubangiji ya mata rahama.

Young Sheikh ya kasance mai karancin shekaru da ke wa'azi a fadin Najeriya wanda jama'a da dama ke ganin ya yi kankanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel