Matar Ɗan Sarkin Ingila, Harry Ta Ji Dadin Najeriya, Ta Ce Ta Samu Gida

Matar Ɗan Sarkin Ingila, Harry Ta Ji Dadin Najeriya, Ta Ce Ta Samu Gida

  • Uwar gidan ɗan Sarkin Ingila, Harry Charles, Meghan Markle ta bayyana Najeriya a matsayin gida da take alfahari da ita a duk inda take
  • Markle ta ce ta ji dadin yadda aka tarbe ta a Najeriya da ta kira kasarta inda ta yi godiya marar misaltuwa kan karban bakwancinsu da aka yi
  • Hakan ya biyo bayan kawo ziyara Najeriya na tsawon kwanaki uku inda suka zagaya wasu jihohi ciki har da hukumar rundunar tsaro da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Matar ɗan Sarkin Ingila, Meghan Markle ta bayyana Najeriya a matsayin gida a gare ta.

Sarauniyar ta bayyana haka ne yayin ziyarar da ta kawo a karshen mako da Yarima Harry Charles inda suka zagaya wurare da dama a Najeriya.

Kara karanta wannan

IMF ta damu kan yadda Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye, ta jero matsaloli

Mai dakin ɗan Sarkin Ingila ta yabawa Najeriya
Matar ɗan Sarkin Ingila, Meghan Markle ta ji dadin tarba daga ƴan Najeriya. Hoto: @datswasup.
Asali: Instagram

Markle ta ji dadin tarba daga Najeriya

A ranar Asabar 11 ga watan Mayu, Markle ta yi taron mata a shugabanci tare da babbar daraktan Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO, Ngozi Okonjo-Iweala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin taron, Markle a cikin wani faifan bidiyo ta ce ta ji dadin ziyarar da suka kawo da mai gidanta, Harry a Najeriya.

Markle ta ce ta ji dadin ziyarar wacce ta kira ta bude ido da kuma ci gaba bayan ta samu karuwa dalilin sanin tushenta.

"Da farko ina son mika godiya kan yadda kuka tarbeni da mijina a wannan kasa, wato kasa ta."
Na ji dadin yadda aka girmama ni da kuma kauna da aka nuna mana, kwanakin da muka kwashe a wannan kasa sun bamu nishadi sosai."
"Abin yabawa ne yadda ake kwatanta matan Najeriya da masu ƙarfin guiwa kuma kyawawa."

Kara karanta wannan

Jami’an Birtaniya sun yi watsi da Yarima Harry a ziyarar da ya kawo zuwa Najeriya

- Meghan Markle

Markle ta ce ta na son Najeriya

Tsohuwar jarumar fina-finan ta ce duk da bikin ranar iyaye da ake yi bata kusa da ƴaƴanta amma ba ta ji komai ba ganin yadda take cikin gida Najeriya cikin ƴan uwa.

Wannan ya biyo bayan kawo ziyara da ɗan Sarkin, Harry ya yi da mai dakinsa zuwa Najeriya na kwanaki uku.

Yayin ziyarar, Harry ya ziyarci jihar Kaduna bayan farawa da hukumar rundunar tsaro a birnin Tarayya, Abuja.

Ɗan Sarkin Ingila, Harry ya zo Najeriya

Kun ji cewa Yarima Harry Charles na kasar Birtaniya da matarsa Meghan Markle za su kawo ziyara Najeriya tun Juma'a, 10 ga watan Mayu.

Rahotanni sun nuna cewa za su kawo ziyarar ne a karkashin gayyatar da hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel