Babban Jigo Kuma Mamban Kwamitin Amintattun PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Babban Jigo Kuma Mamban Kwamitin Amintattun PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Charles Idahosa, tsohon ɗan kwamitin amintattun PDP ya koma jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Edo
  • Tun ranar 29 ga watan Afrilu, 2024, jigon ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da nadamar abin da ya aikata a baya
  • Babban ɗan siyasar ya ce sau uku Gwamna Godwin Obaseki yana yunƙurin murabus saboda wahalar mulkin jihar amma ya hana shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Mamban kwamitin amintattu (BoT) na Peoples Democratic Party (PDP), Charles Idahosa, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a jihar Edo.

Idan baku manta ba, Mista Idahosa, wanda ya kasance na hannun damar Gwamna Godwin Obaseki ya fice daga jam’iyyar PDP a ranar 29 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnan PDP ya ɗauki zafi, ya sha alwashin bincikar Ministan Bola Tinubu

Charles Idahosa da Gwamna Obaseki.
Tsohon mamban BoT a PDP kuma aminin Gwamna Obaseki ya koma APC Hoto: Charles Idahosa, Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Babban jigon ya bayyana cewa abin da yake nadama a lokacin yana cikin PDP shi ne hana Gwamna Obaseki yin murabus sau uku, in ji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban abin da Idahosa ya yi nadama

Ya ce sau uku Obaseki yana faɗa masa cewa ya gaji da wannan mulkin don haka zai sauka daga kujerar gwamnan jihar Edo amma sai ya rarrashe shi ya hana shi.

A cewarsa, duk lokacin da Gwamna Obaseki ya zo masa da zancen murabus ya kan shawo kansa da kalaman ƙarfafa guiwa, tare da faɗa masa dama mulki ya gaji haka.

Idahosa, tsohon babban mashawarcin tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole kan harkokin siyasa, ya faɗi haka ne a gidansa da ke titin filin jirgin sama, Benin, yayin da ake ba shi katin zama ɗan APC.

Charles Idahosa ya zama mamban APC

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Tsohon shugaban PDP ya fadi dalilin takun sakar Wike da Gwamna Fubara

Waɗanda suka halarci wurin sun haɗa da tsohon mataimakin gwamnan Edo, Dakta Pius Odubu, shugabar matan APC ta ƙasa, Mary Alile, sakataren PDP na Edo da sauran jiga-jigai.

Charles Idahosa, na cikin waɗanda suka shiga tawagar Obaseki yayin da ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP a ranar 19 ga watan Yuni, 2020, PM News ta tattaro.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Edo, Sanata Monday Okpebolo, zai yi nasara a zaben gwamnan Edo na ranar 21 ga watan Satumba.

Kotu ta kori ƴan majalisar tsagin Wike

A wani rahoton kuma Ƴan majalisa 27 da ke goyon bayan ministan Abuja sun shiga matsala yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ya dawo ɗanye.

Babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta hana ƴan majalisa 27 bayyana kansu a matsayin mambobin majalisar Ribas har sai ta yanke hukunci.

Kara karanta wannan

PDP ta sake samun nakasu bayan tsohon kakakin majalisa ya fice daga jam'iyyar

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262