Mai Dakin Tinubu Ta Yi Kyautar Ban Mamaki, Ta Rabawa Mutane N500m a Filato

Mai Dakin Tinubu Ta Yi Kyautar Ban Mamaki, Ta Rabawa Mutane N500m a Filato

  • Oluremi Tinubu ta taimakawa mutanen wasu garuruwan da ake ta fama da rigingimu a jihar Filato
  • Uwargidar Najeriya ta yi amfani da gidauniyarta wajen bada tallafin N500m ga dangogi 500 a makon nan
  • Sanata Tinubu ta yi kira ga al’umma su hada-kai domin a cin ma nasara, a daina yin fada da juna

Plateau - A matsayinta na uwargidar shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu, ta bada gudumuwar makudan kudi ga wadanda rikici ya jikkata.

Tashar Arise ta rahoto cewa Sanata Oluremi Tinubu ta bada Naira miliyan 500 ga dangogi 500 da rigima ta auka masu a garuruwan jihar Filato.

Gudumuwar kudin ta shafi mutanen da aka dauko daga kananan hukumomin Mangu, Riyom, Barkin Lado, Bassa, Bokos sai kudancin Jos.

Mai Dakin Tinubu
Shugaban kasa tare da Remi Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Oluremi Tinubu ta ziyarci Jihar Filato

Kara karanta wannan

Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito

Ana sa ran Naira miliyan daya da za a damkawa dangogin da su ka bar garuruwansu a dalilin rigingimu, ya taimaka masu dawowa gidajensu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ta bada gudumuwar ne ta karkashin wata kungiya da ta kafa; Renewed Hope Initiative (RHI), kyautar tsohuwar Sanatar ya jawo mata yabo.

Da aka magana wajen rabon kayan tallafi da bada agajin a birnin Jos da ke jihar Filato a ranar Talata, an ji rikicin ya shafi Bayin Allah da yawa.

Channels ta rahoto Sanata Tinubu wanda mai gidanta ya zama shugaban kasa a Mayu ta ce bambamce-bambamcen da ake da su, su ne karfinmu.

Jawabin da Sanata Tinubu ta yi

"Ina kira ga duka ‘yan Najeriya su rungumi sulhu, juriya, da fahimtar juna yayin da mu ke gina al’ummar da za a zauna lafiya.

Kara karanta wannan

“Aikin Mijinta Ne”: Hotunan Yadda Ayarin Motocin Matar Gwamnan Bauchi Suka Makale a Tabo

Mu tuna da cewa bambamce-bambamcenmu, su ne karfinmu, kuma tare za mu iya shawo kan abuuwan da ke mana barazana.
Ga wadanda abin ya shafa, ina so ku san mu na tare da ku a wannan hali da aka shiga. Baya ga dukiya, mu na taya ku da addu’a."

- Remi Tinubu

Kiran da Remi Tinubu tayi

Kwanaki aka samu rahoto Uwargidan shugaban kasa ta bayyana cewa lokacin cin bulus ya ƙare a ƙasar nan, ta nuna dole a tashi tsaye.

Remi Tinubu ta bayyana cewa ba zai yiwu ƴan Najeriya su kalmashe ƙafa su jira sai an yi musu komai ba, ta roki masu kudi su kawo agaj.

Asali: Legit.ng

Online view pixel