Tinubu Ya Haramtawa Mukarraban Gwamnati Sayen Motocin da Suka Dogara da Fetur

Tinubu Ya Haramtawa Mukarraban Gwamnati Sayen Motocin da Suka Dogara da Fetur

  • A taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a jiya Litinin, Shugaba Bola Tinubu ya haramta sayen motocin da suka dogara da fetur
  • Shugaban kasar ya umarci dukkanin ma'aikatu da hukumomin gwamnati da su koma sayen motocin da ke amfani da iskar gas din CNG
  • A yayin da yake jawabi a taron, Tinubu ya tabbatar da cewa babu ja da baya a sauye-sauyen makamashi da gwamnatinsa ta fara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya haramtawa mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), sayen motocin da suka dogara da man fetur.

Shugaban ya kuma umarci dukkanin ma'aikatu da hukumomin gwamnati da su koma sayen motocin da ke amfani da iskar gas din CNG.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Tinubu ya ba ma'aikatu hukumomi umarni kan motocin CNG
Za a canja dukkanin motoci da janareta da ke amfani da fetur zuwa gas din CNG, in ji Tinubu. Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Twitter

Za a mayar da motocin fetur zuwa CNG

Tinubu ya ba da umarnin ne a taron FEC na jiya Litinin inda ya kuma ba da umarnin fara mayar da motoci da janareta da ke amfani da man fetur ko dizal zuwa gas din CNG.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Cif Ajuri Ngelale, ya kuma tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Ngelale ya bayyana cewa umarnin ya yi daidai da kudurin Tinubu na tabbatar da tsaron makamashi, samar da kayan aiki, da rage yawan amfani da fetur.

Sanarwar an yi mata take da: ‘Shugaba Tinubu ya bada umarnin sayen motocin da ake amfani da gas din CNG.’

"Ba ja baya a harkar makamashi" - Tinubu

Umurnin na ranar Litinin na daya daga cikin manyan shawarwarin da majalisar ta cimmawa kafin ta dage zamanta na sa’o’i hudu zuwa ranar Talata 14 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta hada kai da Enugu domin sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur

A cewar Ngelale:

“Umarnin da shugaban kasas ya bayar zai fara tabbatar da shirin Najeriya na sauya sheka daga fetur da dizal zuwa makamashi mai tsafta a yayin da kuma gas din CNG zai zama mai saukin saye ga 'yan kasa.

A yayin da yake jawabi ga mambobin majalisar zartaswar, Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa babu ja da baya a sauye-sauyen makamashi da gwamnatinsa ta fara.

An kaddamar da gidajen man CNG

A wani lambarin, mun ruwaito kamfanin iskar gas na NIPCO ya kaddamar da sababbin gidajen sayar da gas din CNG a Legas a wani yunkurin daina dogaro da man fetur.

A yayin da zai sayar da lita daya na gas din ga kananan motoci a kan N200, manyan motoci a kan N260, kamfanin ya ce hakan zai karya farashin man fetur da na dizal.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel