Miji, Mata da 'Ya'yansu Biyu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki a Jihar Taraba

Miji, Mata da 'Ya'yansu Biyu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki a Jihar Taraba

  • Magidanci da matarsa da 'ya'yansu biyu sun mutu sakamakon kawo wutar lantarki mai ƙarfi a Jalingo, jihar Taraba
  • Hukumar 'yan sanda ta bayyana cewa wasu mutane da yawa sun samu raunuka kuma suna kwance a Asibiti yanzu haka
  • An ce lamarin ya faru ne bayan na'urar da ke raba hasken wutar ta yi bindiga jim kaɗan bayan dawo da wuta a Anguwar Dinyavoh

Jihar Taraba - Wasu iyalai 'yan gida ɗaya sun mutu sakamakon matsalar wutar lantarki a yankin Dinyavoh da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Jaridar Channels tv ta tattaro cewa waɗanda suka mutu sanadin wutar lantarkin sun kunshi, mahaifi, uwa da 'ya'yansu biyu, yayin da ɗan su ƙarami ɗaya ne kaɗai ya tsira.

Transufoma mai bada hasken wuta.
Miji, Mata da 'Ya'yansu Biyu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki a Jihar Taraba Hoto: channelstv
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Usman Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ƙaramin ɗa na karshe a gidan ya tsallake rijiya da baya.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Ƙara Kashe Mutane a Jihar Sakkwato, 'Yan Sa'kai Sun Fusata Sun Ɗauki Fansa

Jaridar Punch ta tattaro cewa lamarin ya faru ne sakamakon wani tartsatsin wutar lantarki da ya faru da safe biyo bayan fashewar taransfoma a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya shafi gidaje da dama a yankin, inda mutane da yawa suka samu raunuka kuma a halin yanzu suna kwance a Asibiti ana musu magani.

Kakakin ‘yan sandan, a cikin wata sanarwa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin, kuma rundunar ta na zargin cewa wutar lantarki ce ta haddasa.

A kalamansa ya ce:

"A ranar Litinin da misalin karfe 11 na safe, an sanar da mu cewa wani gida da ke unguwar Dinyavoh a Jalingo ya kama da wuta."
“Nan take muka aika jami’an ‘yan sanda na cajo Ofis ɗin GRA zuwa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa, kuma da isar su, sun gano mutanen hudu da wutar lantarki ta ƙona."

Kara karanta wannan

An Samu Asarar Rai Bayan Rufin Wani Gini Ya Rufto a Jihar Taraba

Abinda ya yi ajalin 'yan gida ɗaya

Usman Abdullah ya bayyana waɗanda matsalar wutar ta kashe da Ofonbuk Remond, 44; da matarsa, Mfonbong Remond da kuma 'ya'yansu biyu, Heaven Remond, 15, da First Remond, 13.

Punch ta rahoto kakakin 'yan sandan ya ci gaba da cewa:

“Mun samu bayanai da ke nuna cewa ana dawo da wutan lantarkin nan take na’urar taransfoma da ke aiki a yankin ta fashe."
“Mun samu labarin cewa mafi yawan gidajen unguwar sun samu wutar lantarkin da ta wuce ƙima, wanda hakan ya haifar da barkewar gobarar da ta kone mamatan."

Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazana Ga Shettima, Gawuna da Alkalai a Bidiyo

A wani rahoton kuma Jami'an DSS sun cafke matashiyar nan da ta yi barazanar halaka Shettima, Gawuna da Alƙalan Ƙotun Kano kuma ta kashe kanta.

Fiddausi Ahmadu, 'yar kimanin shekara 23 a duniya ta yi wannan barazana ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Ɗana Tarko, Sun Yi Garkuwa da Babban Jami'in Sojojin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel