Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Dalibai Mata N20,000 Duk Wata

Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Dalibai Mata N20,000 Duk Wata

  • Gwamnatin jihar Kano ta fara biyan ɗalibai mata na jihar tallafin N20,000 duk wata domin bunƙasa karatunsu
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya sanar da fara biyan tallafin karatun ya yi nuni da cewa ɗalibai 45,000 ne za su amfana da shirin tallafin
  • Gwamnan ya kuma bayyana shirin gwamnatinsa na gina sababbin makarantu a ƙananan hukumomin jihar domin kwashe yaran da ba su zuwa makaranta

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta fara bayar da tallafin Naira 20,000 ga ɗalibai mata 45,000 domin tallafa wa ilimin ƴaƴa mata tare da ƙarfafa gwiwar iyaye su tura ƴaƴansu mata zuwa makaranta.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun ƴancin kai wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Kara karanta wannan

Diyyar N30bn: Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotu, Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka

Abba Gida-Gida ya fara biyan dalibai mata N20,000
Gwamnatin jihar Kano ta ba dalibai mata 45,000 tallafin N20,000 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A kalamansa:

"Domin tallafa wa ilimin ƴaƴa mata da kuma kwadaitar da iyaye su tura ƴaƴansu mata zuwa makaranta, muna ba da tallafin Naira 20,000 ga yara mata sama da 45,000 a matsayin shirin gwaji don tallafa musu su ci gaba da karatu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Har ila yau, muna shirin zamu sake kawo tsarin amfani da motocin bas domin jigilar yara mata zuwa makarantu da dawo da su."

Abba Gida-Gida zai gina sabbin makarantu

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin sa tana kuma gina sabbin makarantu a fadin kananan hukumomi 44 a ƙoƙarin da suke yi na ganin sun kwashe duk yaran da ba su zuwa makaranta da ke yawo a kan tituna

Hakazalika, ya nanata ƙudirinsa na tura dalibai 1001 da suka kammala karatun digiri na farko da daraja ta ɗaya zuwa ƙasashen waje domin yin digiri na biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kira Zaman Gaggawa da NLC da TUC a Abuja, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Kano Za Ta Daukaka Kara

A wani labarin na daban kuma, gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu na umartarta ta biya ƴan kasuwa diyyar N30bn.

Wata babbar kotun tarayya dai ta umarci gwamnatin jihar da ya biya ƴan kasuwan da ta rusawa shagunansu a filin masallacin Idi, diyyar N30bn bayan sum maka gwamnatin ƙara a gabanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel