Kotun Ta Ci Taran Abba Kabir Naira Biliyan 30 Kan Rusau A Filin Idi

Kotun Ta Ci Taran Abba Kabir Naira Biliyan 30 Kan Rusau A Filin Idi

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta ci taran Abba Gida Gida kan rusau da ya ke a birnin Kano
  • Kotun wacce ta yanke hukuncin a yau Juma'a 29 ga watan Satumba ta ci taran gwamnan naira biliyan 30
  • Alkalin kotun ya bayyana cewa matakan da gwamnatin ke dauka na rusau jahilci ne da wuce gona da iri

Jihar Kano - Babbar kotun Tarayya da ke jihar Kano ta yanke hukunci kan Gwamna Abba Kabir game da rusau a birnin Kano.

Babbar kotun da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin e a yau Juma'a 29 ga watan Satumba a inda ta ci taran Abba Kabir har biliyan 30 kan rusau a filin Idi.

Kotu ta ci taran Abba Kabir Naira biliyan 30 an rusau
Kotun Ta Ci Taran Abba Kabir Naira Biliyan 30. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Meye kotun ta ce kan Abba Kabir a Kano na rusau?

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: 'Ina Yi Ne Don 'Yan Jihar Kaduna Ba Don Kai Na Ba', Isa Ashiru Ya Bayyana Matakin Gaba

Kotun ta ce za ta yi amfani da kudaden ne wurin biyan diyya ga wadanda abin ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce kudaden za a raba su ga wadanda aka rusa musu kadarori ba bisa ka'ida ba a wurin, cewar Aminiya.

Alkalin kotun, Samuel Amobeda ya kara da cewa matakan da gwamnatin ke dauka jahilci ne da kuma wuce gona da iri.

Tun a farkon hawan Gwamna Abba Kabir ya fara rusau wanda wasu ke ganin bai dace ba inda su ka ce hakan na jawo asarar dukiyoyi.

Wasu mutane sun shigar da kara babban kotun Tarayya don bi musu kadunsu na asarar dukiyoyi, cewar TRT Afirka.

Wane martani Abba Kabir ya yi kan hukuncin?

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun ya bayyana rusau din da rashin bin ka'ida.

Kara karanta wannan

Yadda aka kamo wasu mutum 5 da suka yunkurin siyar da jariri mai kwanaki 8 a Kano

Ya ce:

"Rushe gidajen mutane ba bisa ka'ida ba zalunci ne da keta.
"Dole gwamnati ta biya masu shagunan da abin ya shafa."

Har ila yau, kotun ta haramtawa gwamnatin bayar da filayen ga wasu mutane a nan gaba.

Kwamishinan shari'a a jihar, Barista Haruna Isa ya ce za su daukaka kara don kwatar hakkinsu.

Ya ce ko wane dan kasa ya na da ikon kai kara idan wani abu bai game shi ba, amma tun farko ba a kai karar inda ta dace ba.

Rusau: 'Yan kasuwa sun koma ga Allah a Kano

A wani labarin, 'yan kasuwa da ake rusa musu shaguna a filin Idi da ke jihar Kano sun yi addu'o'i.

'Yan kasuwar sun gabatar da sallar Nafila raka'a biyu da addu'o'in neman taimakon Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel