Peter Obi Ya Tsoma Baki a Rusau Din Kano, Ya Yi Wa Abba Gida Gida Wankin Babban Bargo

Peter Obi Ya Tsoma Baki a Rusau Din Kano, Ya Yi Wa Abba Gida Gida Wankin Babban Bargo

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour ya bayyana matsayarsa game da rushe-rushe da Abba Gida Gida ke yi a Kano
  • A kwanakin nan gwamnatin Kano ta ci gaba da rushe gine-gine da take tunanin ya sabawa dokoki yayin gina su ko mallakarsu
  • Peter Obi ya ce dole a rinka nuna tausayawa ga al'umma ganin yadda rushe-rushen ke jawo asarar dukiyoyi na mutane a jihar

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana cewa wasu rushe-rushe da gwamnatin Kano ke yi za a iya kauce musu da kuma yin uzuri.

Peter Obi ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a ranar Talata 27 ga watan Yuni inda yace ya kamata Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna tausayi ganin yadda mutane ke asarar dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Kano: Dubban Matasa Sun Fito Zanga-Zanga Kan Rusau Da Gwamnatin Abba Gida Gida Ke Yi

Peter Obi ya soki Abba Gida Gida kan rushe gine-gine a jihar Kano
Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam'iyyar Labour, Peter Obi Ya Bayyana Matsayarsa Akan Rusau Na Kano. Hoto: Peter Obi, Vincent News Update.
Asali: Facebook

Obi ya ce yanzu 'yan Najeriya na fama da karancin gidaje wanda ya zama wajibi a duba yanayin da 'yan kasa suke ciki, Legit.ng ta tattaro.

Peter Obi ya bayyana cewa ba a nuna uzuri cikin rusau da ake yi a Kano

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kwanakin nan, akwai rahotanni da ke nuna rushe-rushe da wata gwamnati ke yi saboda rashin bin kai'da da wasu 'yan Najeriya suka yi bisa kuskure.
"Muna da matsalar karancin gidaje na kusan N70m, wasu sun maida gine-gine zuwa gidajensu da wurin kasuwanci ko shaguna.
"Daga cikinsu zai iya yiyuwa ba a basu daman ginin wuraren ba ko kuma sun samu amincewa daga wasu mahukunta."

Ya shawarci Abba Gida Gida da ya bi doka wurin rusau din

Ya kara da cewa:

"Yayin da wasu daga cikin gine-ginen za a iya yi musu uzuri wanda ya jawo asarar dukiyoyi na talakawa da suka yi kuskure da rashin sani ko kuma ba a fahimtar da su da kyau ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Ruguza Gine-Gine, Ta Tsallake Wuraren da Kwankwaso Ya Saida a Kano

"Dole a rinka tausaya wa mutane kuma dole a nuna kulawa ga mutane wurin kawo gyara a daukar irin wannan mataki.
"Ina kira ga gwamnati da ta bi doka wurin daukar mataki ta yadda ya dace."

Abba Gida Gida Zai Sake Gina Shataletalen Tarihi Da Ya Rusa Zuwa Wani Wuri Na Daban A Jihar

A wani labarin, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin sake gina shataletalen da ya rushe kusa da gidan gwamnati.

Rusa wannan shataletale ya jawo kace-nace daga bangarori da dama har ma da magoya bayan gwamnan.

Gwamnati a nata bangaren, ta ce rusa shataletalen an yi shi ne da manufa mai kyau musamman saboda tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel