Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro
- Wata matashiyar budurwa yar Najeriya da masoyinta dan tsurut sun dauka hankali a intanet saboda banbancin halittarsu
- Masoyan sun yi fice a duniya bayan wasu hotunansu na soyayya ya bayyana a dandalin soshiyal midiya, wato TikTok
- Yayin da wasu masu amfani da soshiyal midiya suka yi wa masoyan dariya wasu sun nuna sha'awarsu a gare su
Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya sakamakon bayyana hotunanta tare da sahibinta wanda ya kasance dan tsurut da shi.
Hotunan da shafin @holyson101 ya wallafa a TikTok ya nuna yadda matashiyar ta daga mutumin sama sai kace wani dan karamin yaro.
Yayin da ta dauke shi a dukkan hotunan, wani abu da ya kasance a dukka hotunan shine murmushinsu mai ban sha'awa.
Wani rubutu da ke tattare da hotunan da daya daga cikin masoyan ta wallafa ya ce: "har abadan abada shine muradin babi."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hotunan masoyan ya ja kudi fiye da N253k a daidai lokacin kawo wannan rahoton, inda mutane da dama suka dunga zolayar su.
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin jama'a kan hotunan masoya
Omoyemwen ta ce:
"Kwarai har abadan abada ne muradin domin ke kadai kike da shi ba zai ci amana ba."
user1212214306550 ya ce:
"Pablo da pablet babu wanda zai raba ku za ku tsufa tare da juna."
Chuku-A-Boo-Car ya ce:
"Don Allah wani ya koya mun yadda ake dariya na tsakani da Allah."
Phi_Yin ta ce:
"Har yanzzu akwai soyayya ta gaskiya ke ce kike neman dan yahoo da kamara 3."
Himamah ta ce:
"Akwai miji ke ce kike neman wanda ya hada koma..
"Eh ke."
Afollybaeta ce:
"Muddin dai kuna kaunar junanku❤️Allah ya albarkaci auren."
Unknown ta ce:
"Abun da ya fi komai gayen ba zai samu matsalar fushi ba."
Matashi ya gwangwaje budurwarsa da sabuwar mota, iPhone 15 da fili
A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa ta rusa ihu sannan ta kusa shidewa bayan ta ga sabuwar motar Marsandi da saurayinta ya siya mata a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwarta.
An saka motar kirar Marsandi a cikin wani jan kwali. Ta kusa zaucewa a lokacin da aka mika mata makullin yayin da kawayenta suka bukaci ta saita kanta wuri daya.
Asali: Legit.ng