“Ka Koma Gida Wajen Matarka” Matashiya Ga Magidancin Da Ya Nemi Soyayyarta

“Ka Koma Gida Wajen Matarka” Matashiya Ga Magidancin Da Ya Nemi Soyayyarta

  • Wata matashiyar budurwa ta ki amsa tayin magidanci da ya nemi soyayyarta, tana mai cewa bata ra'ayinsa
  • Mutumin ya yarda cewa yana da aure amma ya furta wa matashiyar so, inda ita kuma ta yi watsi da tayin nasa
  • Wani hoton hirarsu, wanda ya yadu a yanar gizo, ya nuna lokacin da matashiyar ta fada ma mutumin cewa ya koma gida ya hadu da matarsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani magidanci da ya nuna muradinsa na son kasancewa tare da wata matashiyar budurwa ya gamu da tangarda yayin da ta ki amsa tayinsa.

Shafin Postsubman a Twitter ya yada hoton hirar da ya wakana tsakanin mutumin da matashiyar.

Matashiya ta ki amsa tayin soyayyar magidanci
“Ka Koma Gida Wajen Matarka” Matashiya Ga Magidancin Da Ya Nemi Soyayyarta Hoto: Getty Images/@Postsubman. An yi amfani da hoton don misali ne kawai
Asali: Getty Images

A dan takaitacciyar hirar tasu mutumin ya fada ma matashiyar cewa yana da aure. Ya ce amma duk da haka yana ra'ayin kulla wata alaka da ita duk da cewar shi magidanci ne.

Kara karanta wannan

“Ina Girmama Kudi”: Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Dattijo, Ta Nunawa Duniya Shi a Bidiyo

Sam wannan bukata tasa bai yi wa matashiyar ba, wacce ta bukace shi da ya koma gida don kasancewa tare da matarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya fada ma matashiyar cewa yana son kasancewa tare da yarinya mai zafi kamar ta sannan ta amsa masa da:

"Koma gida ka dafa matarka".

Wannan shagube da ta yi masa ya sa yan Twitter da dama yi wa magidancin dariya.

Kalli hirar tasa a kasa:

Masu amfani da Twitter sun yi martani yayin da budurwa ta ki amsa tayin magidanci

@Itz_authority ta ce:

"Ki bar shi ya je ya dafa matarsa, mana. Kowani namij na son auren matar nan da za ta zama matar gida kuma uwa. Amma suna so su ci amana da wannan mai zafin a waje."

@Ladels2 ta yi martani:

"Ki kashe shi, yarinya ke ce bam din."

Kara karanta wannan

Dan Adaidaita Sahu Ya Mayar Da Wayar iphone 14 Pro Max Da Fasinjansa Ya Manta Da Shi, Ya Samu Tukwici

Budurwa yar Najeriya ta yi wuff da wani dattijon bature, hotunansu sun yadu

A wani labari na daban, wata budurwa ƴar Najeriya da ta auri wani bature ta garzaya manhajar TikTok domin ta nuna shi ga mabiyanta.

Sai dai, wasu masu amfani da TikTok sun nuna cewa mutumin ya girmi budurwa nesa ba kusa ba, wanda hakan bai yi mata daɗi ba.

A wani martani da ta yi cikin wani sabon bidiyo, budurwar mai suna Nkeiruka ta gaya wa mutanen da ke sukanta cewa su je su nemo na su mazajen auren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel