Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Masana'anta a Jihar Legas

Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Masana'anta a Jihar Legas

  • An samu tashin wata mummunar gobara a babbar masana'antar sarrafa robobi ta Mega Plastics a jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yamma
  • Mummunar gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 23 ga watan Satumban 2023 inda ta laƙume ɓangaren ma'ajiyar masana'antar
  • Hukumar kashe gobara ta jihar sun yi dirar mikiya a masana'antar domin tabbatar da daƙile gobarar

Jihar Legas - Mummunar gobara ta tashi a wata babbar masana'antar sarrafa robobi ta Mega Plastics a jihar Legas, cewar rahoton jaridar PM News.

Masana'antar sarrafa robobin tana a kusa da kwanar titin Ilupeju a yankin Mushin na jihar Legas.

Mummunar gobara ta tashi a jihar Legas
Mummunar gobarar ta tashi ne da safiyar ranar Asabar Hoto: PMnews.com
Asali: UGC

Jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Legas na can na ƙoƙarin ganin sun kashe gobarar wacce ta tashi a babbar masana'antar sarrafa robobin.

Kara karanta wannan

An tafka asara yayin da gobara ta lamushe fitaccen kamfanin robobi a jihar kasuwanci

Gobarar dai ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 23 ga watan Satumba, da misalin ƙarfe 5:00 na safe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Labarin na zuwa ne a cikin wata sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Hulda da Jama’a da Wayar da Kan Jama’a na Hukumar LASTMA, Adebayo Taofiq, rahoton Punch.

A cewar sanarwar, jami’an LASTMA sun isa wurin da gobarar ta tashi da misalin karfe 6:30 na safe, inda suka tuntubi sauran jami’an bayar da agajin gaggawa don taimakawa wajen kashe gobarar.

Menene musabbabin tashin gobarar?

Yayin da ba a iya gano musabbabin tashin gobara a masana’antar ba, hukumar ta bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa gobarar ta shafi ma’ajiyar kamfanin ne.

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a samu labarin asarar rayuka ba ko raunata a dalilin tashin gobarar wacce ta laƙume ɓangaren ma'ajiyar kamfanin.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Dakarun Sojoji Sun Gano Masana'antar Ƙera Bindigu a Jihar Arewa, Sun Kama Mutum 2

Gobara Ta Lalata Shaguna a Adamawa

A wani labarin na daban kuma, Aƙalla shaguna 14 na hatsi, kayan abinci da sauran wasu kayayyaki suka lalace a dalilin wata gobara wacce ta auku da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Talata, a babbar kasuwar Yola a jihar Adamawa.

Darektan hukumar kashe gobara ta jihar Adamawa, Mr Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa an kashe gobarar ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin jami'an hukumar kashe gobara ta jihar da na hukumar kashe gobara ta tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel