Dalilin Da Yasa Wike Ya Kwace Filayen Peter Obi, BUA Da Sauransu a Abuja

Dalilin Da Yasa Wike Ya Kwace Filayen Peter Obi, BUA Da Sauransu a Abuja

  • Hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta magantu a kan dalilin da yasa ta soke filaye 167 a cikin garin Abuja
  • Hukumar FCTA ta ce mutanen da abun ya shafa sun saba ka’idojin tsarin Abuja ta hanyar kin bunkasa filayen cikin shekaru biyu
  • Abun ya shafi manyan yan siyasa kamar su dan takarar shugaban kasa na LP. Peter Obi da tsohon gwamnan Cross River, Liyel Imoke

FCT, Abuja - Hukumar babban birnin tarayya (FCTA) karkashin jagorancin Nyesom Wike ta bayyana cewa ta soke filayen wasu manyan yan siyasa a Abuja saboda sun ki bunkasa shi.

Ku tuna cewa hukumar FCTA ta sanar da cewar ta soke filaye 167 a fadin yankunan Maitama, Jabi, Gudu da sauran wurare a Abuja.

Wike ya bayyana dalilin kwace filaye a Abuja
Dalilin Da Yasa Wike Ya Kwace Filayen Peter Obi, BUA Da Sauransu a Abuja Hoto: FCTA/Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Wannan yunkuri ya shafi manyan yan siyasa irin su dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, tsohon gwamnan Cross River, Liyel Imoke, Sam Nda-Isaiah, Donubari Josephine Kogbara da Ishaya Baba.

Kara karanta wannan

Abuja: Cikakkun Jerin Filaye 165 Da Ministan FCT Wike Ya Kwace Da Masu Shi

Sauran da abun ya shafa sun hada da Musa Aboki Egu, Hassan Hadejia, Uffot Joseph Ekaette, Shittu Mohammed, Udoma Udo Udoma, Kanu Agabi, Niki Niki Tobi, Ishaku Bello, BUA International, da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FCTA ta yi karin haske kan soke filayen Obi, Imoke da sauransu a Abuja

Da take tabbatar da wannan ci gaban, daraktar labarai da sadarwa na FCTA, Hazat Sule, ta ce an bar filayen ba tare da an bunkasa su ba na tsawon lokaci, wanda hakan yasa basu da wani zabi da ya wuce soke su.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, ya bayyana cewa ka’idar da aka gindaya ita ce, wadanda aka bai wa filayen su bunkasa kadarorin su cikin shekaru biyu bayan ba su shi.

Sule ta bayyana rashin bin wannan tsari na FCTA a matsayin bata tsarin babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sabon Gwamnan CBN Ya Kama Aiki Gadan-Gadan Tare da Mataimaka 4, Bayanai Sun Fito

Wannan ci gaban ya kara tabbatar da sanarwar da Wike ya yi a taron manema labarai na farko bayan rantsar da shi, inda ya bayyana cewa FCTA za ta kwace filaye saboda kawo ci gaba.

Wike ya kuma bayyana cewa ba za a yarda da ayyukan babura ba a babban birnin tarayyar kasar.

Kotun ta tsare wasu matasa 3 kan zargin hayaniya kusa da gidan ministan Abuja, Wike

A wani labarin, mun ji cewa an cafke matasa uku tare da gurfanar da su a gaban kotu kan zargin hayanisa da damun jama'a.

An gurfanar da matasan ne a gaban kotun da ke Lugbe a birnin Tarayya, Abuja saboda tashin hankali da su ka jawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel