Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Ya Ce Za Su Ɗauki 'Yan Sa Kai Don Yaki Da 'Yan Bindigan Jihar

Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Ya Ce Za Su Ɗauki 'Yan Sa Kai Don Yaki Da 'Yan Bindigan Jihar

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da shirinta na ɗaukar 'yan sa kai domin yaki da 'yan bindigar jihar
  • Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook
  • Ya ce hakan wani mataki ne da gwamnatinsa ta ɗauka don ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi jihar

Gusau, jihar Zamfara - Gwamna Dakta Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara, ya bayyana matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka wajen yaƙi da 'yan bindigar da suka addabi jihar na tsawon lokaci.

Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin ranar Talata, 5 ga watan Satumba.

Gwamnatin Zamfara za ta dauki 'yan sa kai
Gwamna Dauda Lawal ya ce za su ɗauki 'yan sa kai don yaki da 'yan bindigan Zamfara. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jihar Zamfara za ta dauki 'yan sa kai don yaki da 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamna Ya Janye Ƙarar da Ya Kai Gwamnan PDP Gaban Kotu, Bayanai Sun Fito

Dauda Lawal ya bayyana cewa bayan tattaunawa da majalisar zartaswa ta jihar ta yi ne suka yanke shawarar ɗaukar 'yan sa kai domin taimakawa jami'an tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wannan wani ƙuduri ne da gwamnatinsa ke da shi na ganin ta kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta ƙo ci ta ƙi cinyewa a faɗin jihar.

A kalamansa:

“A jiya, bayan doguwar tattaunawa da Majalisar zartaswar Jihar Zamfara ta yi a Gusau, gwamnatina ta bayar da umurnin a ɗauki 'yan sa-kai waɗanda za su taimakawa jami'an tsaro a yaƙin da suke yi da 'yan bindiga.”
“Mun yanke shawarar ɗaukan 'yan sa-kai ne saboda kudurin da muke da shi na kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin Zamfara.”

'Yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan bautar ƙasa 8 a Zamfara

A wani labarin na daban, Legit.ng ta yi rahoto kan garkuwa da matasa 8, masu yi wa ƙasa hidima da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Shugaba Ƙasa Ya Tsorata da Abinda Ya Faru a Nijar da Gabon, Ya Ɗauki Matakin Kare Kansa

An bayyana cewa matasan sun taho ne daga birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda suka bi ta jihar Sokoto kafin su gamu da masu garkuwa a yayin da suka shigo jihar Zamfara.

An bayyana cewa mutane 11 ne a cikin motar a yayin da lamarin ya faru, inda uku daga ciki suka samu nasarar tserewa.

An rufe kasuwanni shanu a ƙananan hukumomi 5 na Zamfara

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan rufe kasuwannin shanu biyar da aka yi a wasu ƙananan hukumomin jihar Zamfara guda biyar sakamakon matsaloli na tsaro.

Gwamnatin jihar ta dai ɗauki wannan matakin ne sakamakon yawaitar ayyukan barayin shanu da 'yan fashin daji a ƙananan hukumomin da abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel