Kotu Ta Ba Da Belin Matasa 'Yan Luwadi 69 Da Aka Kama Su Na Auren Jinsi A Delta

Kotu Ta Ba Da Belin Matasa 'Yan Luwadi 69 Da Aka Kama Su Na Auren Jinsi A Delta

  • Babbar kotu a jihar Delta ta ba da belin matasa 69 da ake zarginsu da auren jinsi a karamar hukumar Uvwie da ke jihar
  • Jami’an ‘yan sanda sun kama matsan ne a ranar 27 ga watan Agusta yayin da su ke bikin auren jinsi a garin Effurun
  • Lauyan wadanda ake zargin, Mista Ochuko Ohimor shi ya bayyana haka a ranar Talata 19 ga watan Satumba ga ‘yan jarida

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Delta – Babbar kotun da ke zamanta a Effurun da ke karamar hukumar Uvwie a jihar Delta ta ba da belin wadanda ake zargi da auren jinsi.

Matasan da aka kama su 69 a jihar su na bikin daura aure sun samu beli a jiya Talata kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in Hukumar FRSC Har Lahira, Bidiyo Ya Bayyana

An ba da belin 'yan luwadi 69 a jihar Delta
Kotu Ta Ba Da Belin 'Yan Luwadi 69 A Jihar Delta. Hoto: @DeltaPoliceNG.
Asali: Twitter

Yaushe aka kama 'yan luwadin a Delta?

Jami’an tsaro sun kama matasan ne a ranar 27 ga watan Agusta yayin da su ke bikin auren jinsi da kungiyar su ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan wadanda ake zargin, Mista Ochuko Ohimor shi ya tabbatar da haka a jiya Talata 19 ga watan Satumba da yamma.

CNN ta tattaro lauyan na cewa:

“Wadanda ake zargin an ba da belinsu a kan kudi har Naira dubu 500 da kuma shaidu guda biyu.
“Wadanda za su tsaya musu dole su kasance mazauna Effurun yankin da aka kama matasan a watan jiya.
“Dole kuma wadanda ake zargin su rinka zuwa kotun da ke Effurun don saka hannu a karshen ko wane wata.”

Yadda aka kama 'yan luwadin a Delta

Idan ba a manta ba an kama su ne yayin da su ke auren jinsi inda 'yan sanda su ka tasa keyarsu zuwa ofishin 'yan sanda na Ekpan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jiha A Najeriya Ta Yi Gargadi Ga Jama'a Kan Bullar Babbar Cuta, Ta Ba Da Mafita

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Wale Abass yayin tasa keyar tasu ya yi alkawarin tura su kotu don fuskantar hukunci.

Jami’an tsaro sun kama matasa 'yan luwadi 69 a Delta

A wani labarin, jami’an tsaro sun kai farmaki tare da kama wasu matasa yayin da su ke bikin auren jinsi a jihar Delta.

Matasan an kama su a ranar 27 ga watan Agusta a garin Effurun da ke karamar hukumar Uvwie a jihar.

Hakan ya jawo cece-kuce inda wasu ke ganin an tauye musu hakki na ‘yancin da su ke da shi a matsayin sun a ‘yan kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel