Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da Adamu Bulkachuwa Ya Shigar Kan Hukumar ICPC

Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da Adamu Bulkachuwa Ya Shigar Kan Hukumar ICPC

  • Yunƙurin da tsohon Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi na ganin kotu ta dakatar da binciken da hukumar ICPC ke yi a kansa ya fuskanci koma baya
  • Babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Talata, 19 ga watan Satumba, ta amince da buƙatar hukumar ICPC ta neman tuhumar ɗan majalisar
  • Kotun ta ce Bulkachuwa ba shi da hurumin yin tasiri a kan hukuncin da alƙali zai yanke, don haka ta yi watsi da ƙarar da ya shigar a gabanta

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, a ranar Talata, 19 ga watan Satumba, ta yi watsi da ƙarar da Adamu Bulkachuwa ya shigar.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da Sanatan ya shigar na neman dakatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC, daga bincikensa kan kalaman da ya yi yayin zaman ƙarshe na majalisar dattawa ta 9.

Kotu ta yi watsi da karar Adamu Bulkachuwa
Kotu ta yi fatali da karar Adamu Bulkachuwa kan hukumar ICPC Hoto: Abdulrazaq Garba, Omirhobo
Asali: Facebook

A wani hukunci da ya yanke a ranar Talata, mai shari’a Inyang Ekwo, wanda ya jagoranci shari’ar, ya ce ƙarar ba ta da inganci kuma ya kamata a yi fatali da ita, cewar rahoton TheCable.

Mai shari’a Ekwo ya ce Sanata Bulkachuwa a matsayinsa na ɗan majalisa ya kamata ya san abin da kalaman da ya yi a harabar majalisar dattawan za su jawo masa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shin Adamu Bulkachuwa na da sauran kariya?

Jaridar Punch ta ƙara da cewa, kariyar da mai shigar da ƙara (Bulkachuwa) yake magana a kai ba za ta yi masa aiki ba a wannan shari'ar.

"Haƙƙi ne wanda ya rataya a kan kowane ɗan ƙasa mai bin doka oda wajen taimako da bayar da haɗin kai ga hukumomin a ƙoƙarinsu na sauke nauyon da ya rataya a wuyansu." A cewar alƙalin.

"A wajen da kawai hukumomin tsaro suka take haƙkin ɗan ƙasa wajen gudanar da aikinsu, daga nan akwai buƙatar ɗaukar mataki."

An Katse Min Hanzari, Bulkachuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Bauchi ta Arewa, Adamu Bulkachuwa, ya yi ƙarin haske kan suɓutar bakin da ya yi a majalisar dattawa.

Bulkachuwa ya bayyana cewa ba a bari ya kammala kalamansa ba wanda hakan ya sanya aka yi masa gurguwar fahimtar cewa yana nufin a wasu lokutan yana tasiri kan hukuncin da matarsa ke yankewa a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel