“Abun Takaici”: Babban Lauya Ya Caccaki Sanata Adamu Bulkachuwa Kan Subut Da Baka Da Ya Yi

“Abun Takaici”: Babban Lauya Ya Caccaki Sanata Adamu Bulkachuwa Kan Subut Da Baka Da Ya Yi

  • Wani babban lauyan Najeriya (SAN) bai ji dadin fallasar da Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi kwanan nan ba
  • Da alama baram baramar da dan majalisar ya yi a zauren majalisar dattawa ya taba yancin shari'a a Najeriya
  • A yayin taron rufe majalisar dattawa ta tara, Bulkachuwa ya fallasa cewa yana tursasa matarsa yi wa yan uwansa sanatoci alfarma

Abuja - Yayin da zauren majalisa ta 10 ta fara zangon ta, wani babban lauyan Najeriya (SAN), Jibrin Samuel Okutepa, ya koka cewa shugabannin Najeriya basa mutunta doka.

Kalaman Okutepa sun yi karo da baram baramar da Adamu Bulkachuwa, tsohon dan majalisa daga jihar Bauchi ya yi.

Sanatan Bauchin ya tona cewa yana kutse a hukuncin da matarsa, Zainab ke yankewa lokacin da take aiki a matsayin alkali kuma shugabar kotun daukaka kara, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

“Matata Ta Yi Amfani Da Matsayinta Na Alkali Wajen Taimakawa Sanatoci Yan Uwana,” Sanatan APC Ya Yi Subut Da Baka a Bidiyo

Sanata Adamu Bulkachuwa da Jibrin Samuel Okutepa
“Abun Takaici”: Babban Lauya Ya Caccaki Sanata Adamu Bulkachuwa Kan Subut Da Baka Da Ya Yi Hoto: Sen Adamu Bulkachuwa Muhammad (Senator Adamu Bulkachuwa), Jibrin Sam Okutepa
Asali: Facebook

'Fallasa sirri a talbijin na kasa da zauren majalisa ba sabon abu bane': Okutepa

Furucin ya kuma dasa ayar tambaya a kan martabar Misis Bulkachuwa, domin mutane da dama sun ce ya lalata karfin gwiwar da jama'a ke da shi kan shari'ar Najeriya, jaridar Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana kan hala a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, Okutepa ya soki katsalandan da ake yi wajen gudanar da ayyukan hukuma a kasar.

Ya tuna da wani fallasa da marigayi Sanata Ibrahim Mantu ya yi cewa yan siyasa na taka rawar gari a tsarin zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), inda tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ci bulus.

Ya rubuta a ranar 13 ga watan Yuni:

"Abun bakin cikin Najeriya shine cewa wadanda basa mutunta doka da bin tsari sune ake daurawa bisa kan yan Najeriya domin jan ragamar harkokin kasar. Duba tsarin zabar shugabanninmu.

Kara karanta wannan

Batun jirgin Nigeria Air: Hadi Sirika ya tono asiri, ya ce dan majalisa ya nemi cin hanci

"Kuma saboda haka ne ake ganin munanan ayyukan yan barandar siyasa da fallasar da suke yi kai tsaye na katsalandar a ayyukan hukuma a matsayin ba komai ba. Fallasa sirri ba wani abu bane a talbijin na kasa da zauren majalisa.
"Marigayi Sanata Ibrahim Mantu ya fito fili ya bayyana cewa yan siyasa na taka rawargani a tsarin zabe da INEC. Babu abun da ya faru. Rashawa a fili. Abun takaici."

Ina tursasawa matata yi wa yan uwa na sanatoci alfarma - Sanata Bulkachuwa

A baya mun ji cewa, Adamu Bulkachuwa, sanata mai wakiltan Bauchi ta arewa, ya yi wani gagarumin fallasa game da harkokin matarsa a matsayinta na mai shari'a.

Dan majalisar na Bauchi ya bayyana cewa Zainab Bulkachuwa, matarsa, ta yi amfani da mukaminta a matsayin mai shari'a wajen yi wa takwarorinsa a majalisar dattawa alfarma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng