An Maka Shugaba Tinubu a Kotu Kan Wike Da Wasu Ministoci 6

An Maka Shugaba Tinubu a Kotu Kan Wike Da Wasu Ministoci 6

  • Ƙungiyar SERAP ta maka shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a kotu kan wasu daga cikin ministocinsa
  • Ƙungiyar na neman kotun ta tilasta Shugaba Tinubu ya dakatar da ministocinsa da ke suka taɓa riƙe muƙamin gwamna, karɓar kuɗaɗen fansho
  • SERAP na neman kotun ta kuma tilasta shugaban ƙasar ya sanya su mayar da kuɗaɗen fanshon da suka karɓa daga asusun jihohinsu

Legas - An maka shugaban kasa Bola Tinubu a gaban kotu bisa gazawarsa wajen hana wasu ministocinsa guda takwas, da suka haɗa da Nyesom Wike da David Umahi karbar kuɗaɗen fansho a matsayin tsaffin gwamnoni.

Ƙungiyar SERAP ita ce ta shigar da ƙarar tare da sanya wasu ministoci shida matsayin wadanda ake tuhuma a cikin ƙarar, cewar rahoton PM News.

SERAP ta maka Shugaba Tinubu a kotu
Kungiyar SERAP ta maka Shugaba Tinubu kara a kotu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ministocin su ne Badaru Abubakar, Bello Matawalle, Adegboyega Oyetola, Simon Lalong, Atiku Bagudu da Ibrahim Geidam, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Daga Karshe Jami'ar Jihar Chicago Ta Saki Takardun Shaidar Karatun Shugaba Tinubu

Menene abin da SERAP ke nema a kotu?

A cikin karar mai lamba FHC/L/CS/1855/2023 da ta shigar a ranar Juma’ar a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman kotun da ta tilastawa Shugaba Tinubu ya umarci tsaffin gwamnonin da ke riƙe da muƙamin minista su daina karbar fansho daga asusun jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SERAP na neman kotun ta tilastawa Shugaba Tinubu ya umurci tsaffin gwamnonin da ke riƙe da muƙamin ministoci da su dawo da duk wani kuɗaɗen fansho da kuɗin ritaya da suka karɓa barin aiki ga asusun jihohinsu.

Ƙungiyar ta bayyana cewa gazawar da Shugaba Tinubu ya yi na bai wa tsofaffin gwamnonin da ke riƙe da muƙamin ministoci su daina karbar kuɗaɗen fansho, cin zarafi ne ga rantsuwar da ya yi wajen kama mulki.

Lauyoyin ƙungiyar SERAP, Kolawole Oluwadare da Andrew Nwankwo ne suka shigar da karar a madadin ƙungiyar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumomi 2 Na Tarayya, An Faɗi Sunayensu

Ba a sanya ranar da za a fara sauraron ƙarar ba.

Majalisa Ta Musanta Batun Tsige Akpabio

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa wasu fusatattun sanatoci na shirin tumɓuke Akpabio daga muƙaminsa.

Majalisar ta bayyana cewa ko kaɗan babu shirin raba Godswill Akpabio daga shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel