Majalisar Dattawa Ta Musanta Batun Tsige Godswill Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Musanta Batun Tsige Godswill Akpabio

  • Majalisar dattawan Najeriya ta fito fili ta yi martani kan rahotannin da ke yawo cewa wasu sanatoci na shirin tsige Godswill Akpabio
  • A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar ya fitar a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, ya musanta rahotannin
  • Yemi Adaramodu ya bayyana cewa rahotannin ba komai ba ne face ƙagaggen labari wanda masu ƙoƙarin kawo ruɗani a majalisar ke yaɗa wa

FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, ta yi fatali da rahotannin kafafen watsa labarai na cewa wasu fusatattun Sanatoci na shirin tsige, Godswill Akpabio, shugaban majalisar.

Jaridar Daily Trust ta ce wasu kafafen watsa labarai dai a ranar Asabar, sun fitar da rahoto cewa wasu ƴan majalisar na shirin tsige Akpabio.

Majalisar dattawa ta musanta batun tsige Akpabio
Majalisar dattawa ta ce ba gaskiya ba ne batun tsige Akpabio Hoto: Godswill Obo Akpabio
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa tuni wasu Sanatoci da ba a bayyana sunayensu ba, suka haɗu a Saudiyya domin kammala wannan kuɗirin na tumɓuke Akpabio.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Cikakken Sunayen Yan Majalisar Wakilai Na Labour Party Da Za Su Sake Takarar Zabe

Menene gaskiya kan batun tsige Akpabio?

Sai dai, mai magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana rahoton a matsayin soki burutsu ne kawai, rahoton Premium Times ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Hankalinmu ya karkata kan wata sanarwa mai ɗauke da ayar shaidan a wani sashe na kafafen watsa labarai inda ake yaɗa jita-jita da makircin canjin shugabanci a majalisar dattawa."
"Majalisar dattawan Najeriya tsintsiya ce maɗaurinki ɗaya mai haɗin kai. Wannan soki burutsun hasashe ne da ƙagaggen labarin ƙarya da ƙarairayi na naira miliyan 100 ga kowane ɗan majalisa."
"Yana da kyau a san cewa majalisar dattawa ta 10 a ƙarkashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio, ta gudanar da ayyukanta na doka da kundin tsarin mulki yadda ya dace."
"Muna kira ga ƴan barandan da ke wajen majalisa, waɗanda ke neman kawo ruɗani ta hanyar amfani da kafafen watsa labarai domin datse fika-fikan dimokuraɗiyyar Najeriya, da su shiga taitayinsu."

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Ɗalibar Jami'ar Tarayya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Kasuwa

Majalisar dai a yanzu haka tana hutu, inda za ta dawo a ranar 26 ga watan Satumba.

Sanatoci Za Su Fafata a Zaben Cike Gurbi

A wani labarin kuma, kotunan saurarron ƙararrakin ƴan majalisun tarayya, sun ƙwace nasarar sanatoci guda bakwai a zaɓen 2023.

Huɗu daga cikin sanatocin da aka ƙwace nasararsu, kotunan sun bayar da umarni ga hukumar zaɓe ta INEC da ta gudanar da zaɓen cike gurbi a mazaɓunsu domin tabbatar da wanda ya yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng