Yadda Wani Mutumi Ke Kiwon Kunamai Domin Ya Tatsi Dafinsu, Yana Siyarwa Miliyoyin Kudade

Yadda Wani Mutumi Ke Kiwon Kunamai Domin Ya Tatsi Dafinsu, Yana Siyarwa Miliyoyin Kudade

  • Wani mutum ya bude abin da za a iya kwatanta shi da gonar noman kunamai inda yake kiwon miliyoyin su ya jawo cece-kuce
  • Mutumin mai suna mai kiwon kunamai, ya yada wani faifan bidiyo da ke nuna lokacin da yake tatsar dafin kunamai yana tattarawa a mazubi
  • Dafin kunama shi ne ruwa mafi tsada a duniya, domin galan daya nasa ya kan kudin da basu gaza Naira biliyan 30 ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutum ya nuna yadda ya mallaki gonar kiwon kunamai, inda yake kiwonsu tare da tatsar dafinsu yana kai wa masu bukatar siya.

Mutumin mai suna Scorpion Breeder, ya yada wani faifan bidiyo a kafar TikTok, inda ya nuna gonar kunaman tasa cike da dubban kunamai, idan ma ba miliyoyi ba kuma masu kisa.

A cikin dayan bidiyon da ke shafinsa na TikTok, Scorpion Breeder ya bude wani sashe na musamman, inda ya kuna kunamai suna yawo.

Kara karanta wannan

Wani Batura Ya Canja Dala Zuwa Naira, Ya Siya Shinkafa, Wake Da Kayan Dadi Don More Rayuwa a Najeriya

Ya nuna yadda suke cin abinci har ya taba su kamar dai ya sha maganin da ke hana shi jin karbin karin kunamai.

Mutum mai gonar kunamai ya nuna yadda yake aiki
Gonar kunamai da wani ya mallaka | Hoto: @scorpionbreeder.
Source: TikTok

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu amfani da shafukan TikTok sun yi mamakin ganin gonar, inda da yawa daga cikinsu suka ce sun tsorata da lamarinsa.

Nawa ne kudin dafin kunama?

A cewar majmu’un Encyclopedia Britannica, ana iya sayar da dafin kunama tabbas, kuma shi ne ruwa mafi tsada a duniya. Galan nasa ya kai Naira biliyan 30.

An rubuta a Britannica cewa:

"Dafin kunama yana kai dalar Amurka miliyan 39 a galan daya, wanda ya sa ya zama ruwa mafi tsada a duniya. Ana bukatar tatsar kunama sau miliyan 2.64 don cika galan guda. Dafin kunama yana da tarin a fannin likitanci, kama daga gano cuta har zuwa magance zazzabin cizon sauro."

Martanin jama’a bayan ganin bidiyon

@MEL_16:

“Ina ga ya kamata na tashi na gyara dakina.”

@yo_best_tzuyunista:

“Ji nake kamar wani abu na bin jikina.”

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

@Live Lima865:

“Har na ji kamar an farmaki tunani daga kallon wannan.”

@Karim Khalifa 08:

"Jinjina ga mai daukar bidiyon.”

Yadda wata mata ke cin kyankyasai

A wani labarin, wata mata daga Dar es Salaam a kasar Tanzaniya, ta zama maudu'in tattaunawa a Intanet yayin da aka gano tana kiwon kyankyasai don samun abinci.

Saumu Hamisi, wata mawakiya mai suna Ummy Doll, ta ce mutane sun yi ta maganganu da yawa a lokacin da suka ji tana ajiye kwarin domin ta ci soye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng