Dadi kamar kifi da kaza: Jama'a sun kadu ganin shahararriyar mawakiya na cin kyankyaso

Dadi kamar kifi da kaza: Jama'a sun kadu ganin shahararriyar mawakiya na cin kyankyaso

  • Bayan tafka asara a kiwon kaji da agwagwi, mawakiyar Tanzaniya Saumu Hamisi da ake yi wa lakabi da Ummy Doll ta fara kiwon kyankyasai
  • Ta ce sana’ar sayar da kyankyasai tana da riba mai gwabi, kuma ita da kanta tana son cin kwarin da suke da dandano kamar soyayyen kifi ko kaza
  • Hamisi ta ce da farko ‘yan uwa da makwabta sun yi matukar kaduwa lokacin da ta fara kiwon kwarin amma tun ta fahimtar dasu sun kuma fahimta

Tanzaniya - Wata mata daga Dar es Salaam a kasar Tanzaniya, ta zama maudu'in tattaunawa a Intanet yayin da aka gano tana kiwon kyankyasai don samun abinci.

Saumu Hamisi, wata mawakiya mai suna Ummy Doll, ta ce mutane sun yi ta maganganu da yawa a lokacin da suka ji tana ajiye kwarin domin ta ci soye.

Kara karanta wannan

Babbar magan: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili

'Yar Tanzaniya mai cin kyankyaso
Dadi kamar kifi da kaza: Jama'a sun kadu ganin shahararriyar mawakiya na cin kyankyaso | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Ta ce tana samun kudinta a haka

Ta shaida wa BBC cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wasu sun ce ni mahaukaciya ce amma kyankyasai suna kawo min kudi don haka ban damu da ra'ayin mutane ba."

Hamisi, wacce ke da wata waka mai suna Sina, ta ce kyankyasai na da dadi.

A cewarta:

“Yana daga cikin abincin da na fi so. Za a iya cin su danye, za a iya dafa su da kwakwa ko a hada su da ugali ko shinkafa."

Ta ce kyankyasai kamar kowane abinci ne, kuma suna da dandano kamar na kaza ko soyayyen kifi.

Mawajiyar ta ce ta zabi kiwon kwarin ne bayan ta tafka asara a lokacin da take kiwon kaji da agwagwi.

Kiwon kyankyasai akwai riba

A bangare guda, Hamisi ta yi nuni da cewa kyankyasai da take kiwo sun sha bamban da wanda ake samu a gidaje.

Kara karanta wannan

'Yar aiki ta yi awon gaba da kudi da sarkan N13.9m bayan mako daya kacal da fara aiki

A cewarta:

"Na sayi wadannan ne daga wata cibiya da ke Morogoro. Ba su da cututtuka a jikinsu kuma ina tabbatar da cewa sun rayu a muhalli mai tsafta."

Ta gargadi mutane daga cin kyankyasai da suka samu a zagayen gidajensu.

Hamisi ta kuma bayyana cewa, mafi kyawun yanayin kiyaye kyankyasai shi ne a wuri mai duhu da zafi da kuma samar da isasshen abinci.

Ta ce:

"Suna girma da sauri kuma suna haihuwa da sauri."

Ta ambaci cewa danginta da mabwabtanta sun yi mamaki lokacin da suka sami labarin cewa tana kiwon kyankyasai.

A kalamanta:

"Da farko makwabta da 'yan uwa sun firgita amma yanzu sun saba."

A wani labarin, wasu ma'aurata a garin Kandara da ke Murang'a na kasar Kenya na cikin farin ciki bayan da masu hannu da shuni suka kawo musu dauki bayan shafe shekaru suna rayuwa cikin kunci tare da 'ya'yansu.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

Peter Waweru, wanda ya kwashe shekaru da yawa baya iya motsawa bayan fama da rashin lafiya, yana zaune ne tare da iyalansa a wani gidan da ke daf da rugujewa.

An yi sa'a, wasu mutanen kirki karkashin jagorancin mawakiyar Kikuyu, Anne Lawrence, sun tausaya musu ganin irin mawuyacin halin da suke ciki, inda suka fara fafutukar ginawa Waweru da iyalinsa gida mai mai har ma da bandakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel