Ko ka san irin amfanin nonon kyankyaso a jikin ka?
- Masana sun gano irin amfanin nonon kyankyaso a jikin mutum
- Nonon na kyankyaso na dauke da sinadaran gina jiki da dama
- Daga ciki akwai sukari da sauran kayan da ke gina jikin Dan Adam
Kwanan nan mu ke jin labari cewa ashe Masana sun gano irin amfanin nonon kyankyaso a jikin Dan Adam wanda da dama ba su sani ba.
Nonon kwaron nan da ka sani kyankyaso na dauke da sinadaran gina jiki da dama wanda su ka hada da sukari da kuma sinadarin ‘fats’ mai sa kiba da kuma ‘furotin’ mai gina jiki da kara lafiya kamar yadda wani bincike na Gidan CNN ya nuna.
KU KARANTA: An kashe wani bajimin Farfesa a Najeriya
Ban da wannan ma nonon na kyankyaso na da matukar zaki sannan kuma ga amfani. Wadanda su ka dandana su kace dadin sa kamar abin kwalamar nan na ‘Ice cream’. Nonon kyankyaso dai yana gina jiki Inji wani masani Leonard Chavas da yayi bincike a kai.
Nonon kyankyaso har ta kai ya fi na saniya kara karfi a jikin mutum kwarai da gaske. A sauran kasashe dai ana kokarin ganin yadda za a rika gyara nonon kwaron ne.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng